2027: Tarihin Shugabannin Jam'iyyar Hadaka Ta ADA da Su Atiku ke Son Kafawa

2027: Tarihin Shugabannin Jam'iyyar Hadaka Ta ADA da Su Atiku ke Son Kafawa

  • Sabuwar jam’iyyar ADA da ake shirin kafawa ta bayyana Akin A. Ricketts a matsayin Shugaban riko, yayin da Abdullahi Musa Elayo zai zamo sakatare
  • Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ne ya jagoranci taron da ya tabbatar da kafa jam’iyyar tare da kaddamar da kwamitin mutum 15
  • Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ne shugaban kwamitin sabuwar jam'iyyar, yayin da Dr Umar Ardo ke matsayin sakataren kwamitin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gamayyar 'yan adawa a Najeriya sun bayyana shirin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa ta ADA, wadda ke da burin karbe mulki daga hannun shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Taron da aka gudanar a Abuja karkashin jagorancin Sanata David Mark, ya zayyana cewa jam’iyyar ADA ce za ta zama sabuwar hanyar hada kan adawa.

Shugabannin riko na ADA a Najeriya
Umar Ardo da Akin Ricketts da za su jagoranci ADA a Najeriya. Hoto: @Wildman477|@Imranmuhdz
Asali: Twitter

Tribune ta wallafa cewa Akin A. Ricketts da ya fito daga jihar Cross River ne zai zama shugaban riko na jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin shugaban ADA na rikon kwarya

Taron ya amince da nada Cif Akin A. Ricketts a matsayin shugaban jam’iyyar na riko, inda zai jagoranci shirye-shiryen tsarin mulki da kafuwar jam’iyyar.

Akin A. Ricketts dan siyasa ne da ya fito daga jihar Cross River kuma ya rike mukamai da dama a tarihinsa.

Ricketts ya kasance dan jam'iyyar APC kuma ya yi takarar Sanata a Cross River a APC a 2023 bayan ya rike shugaban kwamitin gudanarwa na NPA a lokacin Muhammadu Buhari.

Rahoton Business Day ya nuna cewa Cif Akin A. Ricketts ya taba rike kwamishinan yada labarai na jihar Cross River.

Waye sakataren riko na ADA a Najeriya?

Abdullahi Musa Elayo, wanda aka dade yana fafutuka a harkar siyasa, shi ne zai rike matsayin sakataren jam’iyyar na riko.

Bincike ya nuna cewa Abdullahi Musa Elayo gogaggen lauya ne da ya fito daga jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Shafin tarihi na Blerf ya bayyana cewa Hon. Abdullahi Musa Elayo ya yi karatu a jami'ar ABU Zariya kuma ya yi aiki a jihar Filato.

Bayani kan Rotimi Amaechi da Umar Ardo

A cikin jawabin da aka fitar, an bayyana kafa kwamitin mutum 15 da zai daura jam’iyyar ADA a kan hanya.

Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri, Hon. Chibukwe Rotimi Amaechi, ne shugaban kwamitin sabuwar tafiyar siyasar.

Dr Umar Ardo da ya jagoranci kafa kungiyar Arewa ta LND kuma tsohon hadimin shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zama sakataren shi.

Bincike ya nuna cewa Umar Ardo ya yi takarar gwamna a jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2023.

Manyan 'yan adawa yayin wani taro a Abuja
Manyan 'yan adawa yayin wani taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sauran manyan 'yan siyasa da suka hada da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da David Marka na cikin jagororin tafiyar.

Ministan Tinubu ya soki kafa jam'iyyar ADA

A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festur Keyamo SAN ya yi martani ga masu kafa jam'iyyar ADA.

Festus Keyamo ya ce babu alamar hadakar jam'iyyu a sabuwar tafiyar da aka kawo, kuma kafa jam'iyya ba sabon abu ba ne a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa babu wata alama da ke nuna cewa sabuwar tafiyar za ta yi wani tasiri kamar yadda APC ta yi a zaben 2015.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng