'Yan APC Sun Taso Ganduje a Gaba, Sun Masa Ihu a Taron Jam'iyya a Gombe

'Yan APC Sun Taso Ganduje a Gaba, Sun Masa Ihu a Taron Jam'iyya a Gombe

  • A yau Lahadi aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na APC a Gombe inda aka samu zaman dar-dar sakamakon rashin jituwa tsakanin jiga-jigan jam’iyyar
  • Faifan bidiyo ya nuna yadda aka yi wa Abdullahi Ganduje ihu da turereniya yayin da bayyana goyon baya ga Bola Tinubu
  • Wasu wakilai sun fusata da yadda aka yi watsi da Kashim Shettima, sun yi zage-zage da tayar da hankali, alamar rikici na shirin barkewa a 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya.

Taron ya gudana ne a babban dakin taro da ke birnin Gombe a yau Lahadi 15 ga watan Yunin 2025.

Yadda aka yi wa Ganduje ihu a taron APC
An yi wa Ganduje ihu a taron APC a Gombe. Hoto: Ganduje Media for Tinubu.
Asali: Facebook

Taron APC ya rikide zuwa tashin hankali

Wani faifan bidiyo da @Galafi_Hamma ya wallafa a X ya nuna yadda ake yiwa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ihu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan bai rasa nasaba da rigimar da ta ɓarke yayin taron saboda wasu bambance-bambance da aka samu.

Lamarin ya faru ne bayan da mataimakin shugaban jam’iyya na kasa a yankin, Kwamred Mustapha Salihu yake nuna goyon baya ga Bola Tinubu a 2027.

Taron wanda aka gudanar a Jihar Gombe, ya samu halartar kusan duka ministoci, ‘yan majalisa da gwamnonin jam’iyyar daga yankin.

Musabbabin rigima a taron APC a Gombe

Abdullahi Ganduje, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya jagoranci wasu manyan jiga-jigai zuwa wajen taron.

A lokacin da Salihu ya yi jawabi, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu don ya zama dan takara daya tilo, amma bai ambaci Shettima ba.

Majiyoyi sun ce hatsaniyar ta fara ne bayan jawabai da aka yi na nuna goyon bayan Bola Tinubu.

Sai dai an ce an ki ambaton mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima tare da Tinubu.

Hakan bai yi wa wasu daga cikin wakilai a garin dadi ba inda suka fada zage-zage da kokarin kawo hargitsi a taron.

Taron APC ya koma rikici a Gombe
Abdullahi Ganduje ya ci karo da matsala taron APC. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Bidiyon abin da ya faru da Ganduje

A saman bidiyon, matashin ya rubuta cewa wannan alama ce da ke nuna za a samu matsala zaben 2027 da Bola Tinubu.

Ya ce:

"Kalli yadda jama’a ke daga murya suna ihu da cewa 'Ba ma yi', ma’ana “Ba mu goyon baya” yayin da suke ture Ganduje a wani taron APC.
"Wannan abin kunya ne da kuma kin mubaya'a ga Tinubu da abokan siyasarsa.

Dan APC ya tattauna da Legit Hausa

Hon. Musa Adamu ya ce ya kamata a kawo karshen rikicin da jam'iyyar ke fama da ita.

Adamu ya ce maganar sauya Kashim Shettima ba ta taso ba saboda jigo ne a Arewa maso Gabas.

Ya ce:

"Dole a zauna a kawo wannan rikita-rikita idan ba haka ba APC za ta iya samun matsala."

Ya ce abin takaici ne yadda wasu suka tayar da kura da neman jawowa Shettima bakin jini a Gombe.

Gwamna Inuwa ya ba Tinubu tabbaci a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Inuwa ya bayyana haka ne yayin wani taro a Gombe inda ya ce Tinubu ya yi abin da ba a taba gani ba a jihar tsawon shekaru da suka wuce.

Gwamnan ya ba shugaban tabbacin cewa Gombe ta shi ce kuma za su goya masa baya, su raka shi filin yaki domin nasara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.