Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kwara, Sun Kashe Masu Ibada

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kwara, Sun Kashe Masu Ibada

  • ‘Yan bindiga sun kashe masu ibada uku tare da sace mutane 15 yayin zaman addu’ar dare a kauyen Ekerin da ke karamar hukumar Ekiti ta Kwara
  • Maharan sun kutsa wurin ibadar ne da dare, suna harbe-harbe ba kakkautawa kafin su kashe wasu mutane sannan suka yi awon gaba da sauran bayin Allah
  • Rundunar ‘yan sandan Kwara ta tabbatar da harin, tana cewa an tura jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace da cafke maharan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ilorin, Kwara - Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace masu ibada 15 a daren Asabar 23 ga watan Mayun 2026.

Majiyoyi suka ce yan bindiga sun kai hari ne yayin zaman addu’a a wajen kauyen Ikiran da ke karamar hukumar Ekiti, Kwara.

Yan bindiga sun kashe masu ibada a coci
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni daga Tribune sun bayyana cewa lamarin ya faru ne wajen karfe 10:30 na dare a cibiyar ibada ta Ijo Ajaye Ati Igbala da ke kauyen Ekerin.

Kara karanta wannan

Benue: Ƴan bindiga sun yi yunkurin kai hari a wurin zaben fitar da gwani na APC

Yadda mahara suka farmaki masu ibada

An ce mahara dauke da makamai sun mamaye filin addu’ar, suna harbe-harbe ba kakkautawa, inda suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da wasu 15.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da harin tare da bayyana cewa an fara aikin ceto cikin gaggawa.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana harin a matsayin mugun aiki mara tausayi da aka kai kan bayin Allah marasa laifi da ke gudanar da ibada cikin lumana.

Sanarwar ta ce Fasto Adebayo Abiodun ne ya kai rahoton cewa ‘yan bindiga sun kai hari wurin addu’ar Ori-Oke Ijaye ta kauyen Ekerin ranar Asabar.

Yan bindiga sun cafke masu ibada 15 a Kwara
Babban sufeta-janar na ƴan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Abin da jami'an ƴan sanda suka yi

Bayan samun rahoton gaggawa, jami’in ‘yan sanda na yankin Ekiti ya tattara jami’ai tare da tura su wurin domin daukar matakan tsaro cikin hanzari.

Kwamishinan ‘yan sandan Kwara, Ojo Adekimi, ya umarci fara aikin hadin gwiwar jami’an tsaro, masu leken asiri da tawagar jirgin sama marar matuki.

Kara karanta wannan

Ana shirin babbar salla, 'yan bindiga sun yi fashin ragunan layya a Kano

Ya bayyana harin a matsayin dabbanci mara imani, yana tabbatar wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa rundunar za ta kubutar da wadanda aka sace.

Rundunar ta ce ana ci gaba da sintiri cikin dazuka, tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro domin gano maharan tare da hukunta su, cewar Punch.

An bukaci mazauna karamar hukumar Ekiti da sauran jama’ar Kwara su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai masu amfani.

Yan bindiga sun farmaki Yan sanda a Kwara

A wani labarin, an ji cewa yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani sansanin 'yan sanda a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka jami'an 'yan sanda tare da raunata wasu yayin harin wanda suka kai da safe.

Kwamoshinan 'yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa jami'an da suka ji rauni na samun kulawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com