'Abu 1 da Zai Hana Jam'iyyun Adawar Najeriya Su Haɗa Kansu kafin Zaɓen 2027'

'Abu 1 da Zai Hana Jam'iyyun Adawar Najeriya Su Haɗa Kansu kafin Zaɓen 2027'

  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa jam'iyyun adawa ba za su taɓa haɗa kai ba matukar suka ci gaba da sukar manufofin gwamnatin Tinubu
  • Shugaban Majalisar Dattawan ya ce kamar yadda Shugaba Tinubu ya faɗa, yana fatan ƴan adawa su daidaita kansu kafin 2027
  • Akpabio ya bukaci jam'iyyun adawa da su yi kokarin sasanta kansu kafin zaɓen 2027 domin kada su samu dalilin fakewa idan sun sha ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya hango abin da zai iya zama alaƙaƙai ga haɗakar jam'iyyun adawa a Najeriya.

Sanata Akpabio ya ce jam’iyyun adawa ba za su iya hada kai ko daidaita kansu ba matukar suka ci gaba da sukar komai dangane da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Akpabio ya ce sukar gwamnatin Tinubu kaɗai ta isa hana jam'iyyun adawa zaman lafiya Hoto: @AkpabioSen
Asali: Facebook

Akpabio ya fadi hakan ne a ranar Juma’a, yayin kaddamar da sabuwar hanyar mota da aka gina a birnin tarayya Abuja, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ‘yan adawa irin su tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da na Ekiti, Ayo Fayose, sun halarci wurin kaddamar da sabon titin.

APC na kokarin maida Najeriya tsarin jam'iyya 1?

Ya tunatar da kalaman da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Dimokuraɗiyya, lokacin da ya yi jawabi a gaban zaman haɗin gwiwa na Majalisar Ƙasa a ranar Alhamis, 12 ga Yuni, 2025.

A lokacin, Tinubu ya musanta zargin cewa APC na kokarin hana jam’iyyun adawa numfashi ko maida Najeriya kasa mai jam’iyya daya.

Haka nan kuma, shugaban ƙasa ya ce yana farin ciki da ganin jam’iyyun adawa na fama da rigingimun cikin gida.

Akpabio ya bukaci ƴan adawa su haɗa kansu

A rahoton Leadership, Akpabio ya ce:

“Kamar yadda shugaban ƙasa ya ce, ba ya son Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya daya.Yana addu’a tare da fatan cewa jam’iyyun adawa su daidaita kansu. ku yi kokarin daidaita kanku kafin zaɓe na gaba domin kada ku zo kuna zargin mu muka hana ku kataɓus."

“Amma idan kuna tsammanin ni a matsayin wakilin shugaban kasa kuma shugaban majalisar dattawa zan sasanta ku, to wallahi ba zan yi hakan ba.”
“Shi ya sa shugaban kasa ya ce yana fatan ku haɗu kanku, amma idan ba za ku haɗu ba, ba zai taimaka muku ku haɗa kai ba. Wannan siyasa ce.”

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce matukar ƴan adawa za su ci gaba da ƴaɗa ƙarya ta hanyar sukar duk wani motsin gwamnati, to ba za su yaɓa haɗuwa wuri ɗaya ba.

Akpabio da Shugaba Tinubu.
Shugaban Majalisar Dattawa ya ce yana fatan ƴan adawa su daidaita kansu kafin 2027 Hoto: @NGrSenate
Asali: Twitter

Wani mai goyon bayan Atiku kuma ɗan PDP, Kabir Rabiu ya shaida wa Legit cewa ko da maganganun da suke faɗa ba su kai zuciya ba, ƴan adawa za su shirya su karbi mulki a 2027.

Matashin ɗan siyaaar ya ce:

"Da wuya idan waɗannan maganganun sun kai zuci, amma ni a ganina wannan alama ce da ke nuna sun firgita da shirin da Atiku ke yi na haɗa maja.

"Idan ba tsoro suke ji ba, meyasa kwana biyun nan suke ta magana a kai? Tinubu, Wike yanzu ga Akpabio, in sha Allahu sai mun ga bayan APC a 2027.

Majalisa ta sauya tsarin ranar dimokuraɗiyya

A wani labarin, kun ji cewa Majalisa ta amince ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar da shugaban ƙasa zai riƙa yin jawabi a gabanta kowace shekara.

Hakan na nufin shugaban ƙasa zai riƙa bayyana a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai domin yin jawabin ranar dimokuraɗiyya a kowace ranar 12 ga Yuni.

An yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis yayin zaman haɗin guiwa wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262