Asiri Ya Tonu: ICIR Ta Fallasa 'Boyayyun Dalilan' Tinubu na Tsige Ministoci 2
- A ranar 21 ga Afrilun 2026 ne Shugaba Bola Tinubu ya tsige ministan kudi, Wale Edun da kuma ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa
- A lokacin Wale Edun, an samu matsalar raba kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa, inda ma'aikatar lafiya ta samu naira miliyan 36 kacal cikin naira biliyan 218
- Cibiyar bincike da wallafa rahotanni ta ICIR ta bankado wasu manyan dalilai da ta ce su ne suka sanya Tinubu ya tsige ministocin biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da gagarumin garambawul a majalisar zartarwa ta tarayya, inda ya tsige ministan kuɗi, Wale Edun, da takwaransa na Ma'aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane, Ahmed Dangiwa, a ranar Talata.
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ke fuskantar matsin lamba kan yadda ake tafiyar da tattalin arziƙin ƙasa da kuma tsadar gidaje a Najeriya.

Source: UGC
'Rashin lafiya ta sa aka tsige Edun'
Binciken da cibiyar The ICIR ta gudanar ya nuna cewa, sallamar Wale Edun ba ta rasa nasaba da taɓarɓarewar lafiyarsa.
Wata majiya mai tushe ta bayyana wa ICIR cewa, tun a ƙarshen shekarar da ta gabata Edun ya so ya ajiye aiki domin ya kula da lafiyarsa, amma Tinubu ya nemi ya ɗan jira har sai an samu wanda zai maye gurbinsa.
Duk da cewa ana kallon Wale Edun a matsayin aminin Shugaba Tinubu, masana sun bayyana cewa, a lokacin da yake minista, ya fuskanci ƙalubale da dama.
Kunle Olubiyo, wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya bayyana fannin kuɗi a ƙarƙashin Edun a matsayin "fannin da ya rushe ba tare da alamar farfadowa ba."
Matsalolin da Edun ya samu a minista
Manyan matsalolin da Wale Edun ya samu a matsayinsa na minista sun haɗa da:
1. Rashin tsarin kasafin kuɗi:
A lokacin Edun, an samu aiwatar da kasafin kuɗi har guda huɗu (2023, 2023 (kari), 2024, da 2025) a lokaci guda, wanda hakan ya saɓa wa dokar lissafin kuɗi.
2. Matsalar ma'aikatar lafiya:
An kasa fitar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa, inda ma'aikatar lafiya ta sami naira miliyan 36 kacal daga cikin naira biliyan 218 da aka ware mata, wanda hakan ya shafi riga-kafin yara.
3. Matsalar farashin mai da lantarki:
Akwai korafi kan rashin wutar lantarki da kuma ƙarin farashin man fetur da kashi 65 cikin ɗari duk da fara aikin matatar mai ta Dangote, wanda aka alakanta da ma'aikatar kudi, kan zargin kasa tsara yadda tattalin zai bi da wadannan fannoni.
Sai dai, Edun ya taimaka wajen ƙarfafa asusun ajiyar ƙasar na waje zuwa dala biliyan 40, da kuma samar da rarar kuɗaɗen kasuwanci da bunƙasar tattalin arziƙi (GDP).

Source: Twitter
Gazawar Dangiwa a ma'aikatar gidaje
A ɓangaren Ahmed Dangiwa kuwa, rahotanni sun nuna cewa ya kasa cike gibin gidajen da ake buƙata a Najeriya, in ji rahoton Leadership.
Dangiwa da kansa ya taɓa bayyana cewa ana buƙatar gina gidaje dubu 55 a kowace shekara har tsawon shekaru 10, wanda hakan zai ci naira tiriliyan 5.5, amma kasafin kuɗin da aka ba shi bai kai hakan ba.

Kara karanta wannan
Yadda rikicin Iran ya buɗe kasuwar man Najeriya, ƙasashen Turai sun zo neman agaji
Haka kuma, an sami matsalar sarrafa filaye da rashin samun bashi ga talakawa domin gina gidaje sakamakon hauhawar ruwan bashi.
Sakamakon haka, an naɗa Muttaqa Rabe Darma a matsayin wanda zai maye gurbinsa. An ba dukkan tsofaffin ministocin wa'adin zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026, domin su miƙa ragamar ofisoshinsu.
Martanin Dangiwa bayan an tsige shi
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan gidaje, Ahmed Dangiwa, ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi na yi wa ƙasa hidima.
Dangiwa ya bayyana cewa ya yi amfani da lokacinsa a matsayin minista wajen bayar da gudunmawar tabbatar da nasarar "Renewed Hope Agenda."
Yayin da yake shirin miƙa ragama, tsohon ministan ya lissafa wasu daga cikin manyan nasarorin da ya samu a shekarun da ya yi kan kujerar daga Katsina.
Asali: Legit.ng

