Batutuwan da Tinubu Ya Tabo a Jawabin Ranar Dimokuradiyya a Majalisa

Batutuwan da Tinubu Ya Tabo a Jawabin Ranar Dimokuradiyya a Majalisa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki a ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya
  • Ya bayyana irin rawar da majalisa ta taka wajen kare demokuraɗiyya, musamman a lokutan ƙalubale kamar na yunƙurin wa’adin mulki na uku a 2006
  • Tinubu ya kuma yi alkawarin cewa ba zai taɓa goyon bayan kafa gwamnatin jam’iyya guda ba a Najeriya duk da rade radin da ake yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin cigaban demokuraɗiyya a Najeriya tun daga 1999, tare da bayyana irin gudunmawar da majalisa ta bayar wajen kare tsarin.

Tinubu ya ce Najeriya ta fice daga mulkin soji zuwa tafarkin demokuraɗiyya mai inganci, inda ya yabawa ‘yan majalisa bisa irin rawar da suka taka wajen tabbatar da gaskiya.

Bola Tinubu ya yi jawabi a majalisa
Tinubu ya musa zargin mayar da Najeriya karkashin jam'iyya daya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanin da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana cewa zaman majalisar ya kasance wani bangare na bikin ranar Dimokuraɗiyya, inda ya yi amfani da damar wajen bayyana halin da ƙasar ke ciki.

Dimokuradiyya: Tinubu ya yabawa majalisa

Shugaban ƙasa ya kawo misalai da dama na irin yadda Majalisar Tarayya ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin mulki, musamman lokacin da Janar Sani Abacha ya rusa majalisa a 1993.

Ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisa, ciki har da Sanata Ameh Ebute, sun ƙi yarda da hakan har aka kulle su.

Ya ambato yadda Majalisar ta biyar ta hana yunƙurin wa’adin mulki na uku a 2006, da kuma yadda aka bai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, damar rike mulki a 2010.

Tinubu ya musanta zargin zama karkashin jam’iyya 1

Bola Tinubu ya karyata zargin cewa yana da niyyar kafa jam’iyya ɗaya da ke mulki a fadin Najeriya.

Shugaban ya ce:

“Na taɓa yaki da tsarin jam’iyya guda tun kafin in zama shugaban ƙasa, kuma har yanzu ban yarda cewa hakan na da amfani ga ƙasa ba.”

Ya ce zargin yana fitowa ne daga masu tsoro da suke cikin ruɗani, yana mai tabbatar da cewa ya kasance mai girmama tsarin siyasa da bayyana ra’ayi.

Tinubu ya ce ya habaka tattalin Najeriya
Tinubu ya ce ya habaka tattalin Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Maganar Tinubu kan habaka tattalin Najeriya

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki domin gyara tsarin da ya yi tsami, ciki har da shirin gyaran haraji domin ƙarfafa tattalin arzikin gida.

Ya yaba da matakin majalisa na nazari da amincewa da dokokin da suka shafi gyaran haraji, yana mai fatan sanya su hannu a kansu a nan kusa.

A karshe shugaban ya karrama wasu mutane da ya ce sun bayar da gudumawa wajen kafa dimokuradiyya a Najeriya, ciki har da Shehu Sani da Uba Sani.

Zanga-zangar goyon bayan Tinubu a jihar Benue

A wani rahoton, kun ji cewa an yi zanga zangar goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Benue.

Matasan da suka fito zanga zangar sun nuna amincewa da salon mulkin Bola Tinubu, inda suka ce yana kan daidai.

Matasan sun fito zanga zangar ne yayin da wasu 'yan Najeriya suka fito kan tituna a wasu joihohi suna korafi kan salon mulkin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng