"Arewa Ta fi Kowacce Shiyya Morewa," Dankabo Ya Fadi Yadda ake Amfana da Tinubu
- Dan kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu a 2023, Ahmed Dankabo ya ce yankin Arewa ya fi kowa amfana da manufofin gwamnati
- Ya ce cire tallafin man fetur da daidaita canjin kuɗin waje matakai ne masu amfani da za su inganta rayuwar talakawan Najeriya
- Dankabo ya jaddada cewa yunƙurin Tinubu na ba kananan hukumomi cikakken iko zai taimaka wajen inganta shugabanci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ahmed Dankabo, ɗan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023, ya ce Arewa na amfana sosai daga manufofin sauyi na Bola Tinubu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar domin tunawa da ranar Dimokuraɗiyya ta 2025, Dankabo ya bayyana nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen 2023 a matsayin wani babban sauyi ga Najeriya.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Dankabo ya ce kuri’ar da 'yan Najeriya suka ba Tinubu a zaɓe, alama ce ta yarda da jagorancin kwarai da hangen nesan Shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dankabo ya yabi kudirorin Bola Tinubu
Vanguard ta ruwaito Dankabo ya bayyana cewa tabbacin da yake da shi game da ƙwarewar Tinubu wajen sauya Najeriya.
Ya ce:
“A wancan lokacin na san cewa Najeriya na buƙatar jagora mai ƙarfin gwiwa da hangen nesa. Ina alfahari da cewa na sadaukar da lokacina da ƙarfina a wani aiki da yanzu haka ya fara haifar da ɗa mai ido ga 'yan Najeriya.”
Ya yaba da yadda shugaban ƙasa ke tafiyar da gwamnati, yana ambato cire tallafin fetur da daidaita farashin musayar kuɗi a matsayin matakai masu wahala amma masu amfani.
“Tinubu yana ƙoƙari,” in ji Dankabo.
Dankabo ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauyen suna da muhimmanci wajen daidaita tattalin arzikin ƙasa da hana ƙasar faɗawa cikin matsanancin matsi.
Ya ce:
“Da ba don shugabancin Tinubu mai ƙarfin hali ba, da Najeriya tana fuskantar barazanar durƙushewa ta fuskar kuɗi.”
Dankabo ya ce yankin Arewa shi ne yafi kowa amfana daga manufofin shugaban ƙasa da kuma mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa.

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa yunƙurin ba kananan hukumomi cikakken 'yanci a ƙarƙashin shugabancin Tinubu zai ƙarfafa dimokuraɗiyya a matakin ƙasa.
Ya bayyana manyan ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a sassan Arewa a matsayin wani ɓangare na gagarumar gudunmawar gwamnatin Tinubu.
Tinubu ya fadi fatansa kan yan adawa
A baya, kun ji shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce yana fatan yan adawa da suka aminta da tafiyar APC su ci gaba da sauya sheka, kuma za a karbe su hannu bibbiyu
Bola Tinubu Ya bayyana haka ne a yayin jawabinsa kan ranar dimokuraɗiyya da ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar nan a ranar 12 ga watan Yuni, 2025.
Ya kafa da cewa ba alhakinsa ba ne ya taimakawa yan adawa su gyara matsalolin cikin gidansu ba, duk da a cewarsa, ba shi da niyyar mayar da Najeriya kan tsari daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng