Jawabin Tinubu Ya Harzuka 'Yan Adawa, Atiku, Obi, PDP, SDP, ADC Sun Masa Rubdugu
- Jam’iyyun adawa da suka hada da PDP, ADC da SDP sun soki Shugaba Bola Tinubu kan furucin cewa yana farin ciki da rikicin da ke cikin gidajensu
- Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga Majalisar Tarayya yayin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce jam’iyyun adawa su gyara gidajensu
- Jam’iyyun sun zargi gwamnati da hannu wajen tayar da rikici a cikin su, suna masu cewa hakan ya nuna yunƙurin kafa gwamnati ta jam’iyya guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyun adawa a Najeriya sun caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa furucinsa da ya bayyana farin cikinsa kan rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyunsu.
Shugaban Najeriyan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da yake jawabi ga zaman haɗin gwiwar Majalisar Tarayya, inda ya ce ba zai iya gyara gidajen jam’iyyun adawa ba.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyun adawan kamar PDP, ADC da SDP sun bayyana furucin Tinubu a matsayin nuna tsoro da yunƙurin karya tsarin siyasa na faɗin ra’ayi a ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin ADC kan furucin Bola Tinubu
Shugaban ADC na ƙasa, Dr. Ralph Nwosu, ya bayyana cewa furucin Tinubu abin takaici ne daga mutumin da ke rike da madafan iko, musamman duba da tarihin gwagwarmayarsa a mulkin soja.
Ralph Nwosu ya ce:
“Gwamnati na amfani da dukiyar ƙasa wajen dakushe adawa tare da yunƙurin kafa jam’iyya guda da ta fi mulkin soja tsauri.”
Nwosu ya kara da cewa jam’iyyun adawa na shirya haɗin gwiwa domin fuskantar APC a 2027, inda ya yi alkawarin cewa za a nuna musu karfi a zaɓe mai zuwa.
PDP: "Za a kifar da Tinubu a zaben 2027"
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya ce Tinubu zai sha mamaki a zaɓen 2027 saboda halin da ‘yan Najeriya ke ciki na ƙuncin rayuwa.
Ya ce:
“Bayan babban taron da ke tafe, PDP za ta dawo da karfinta. APC za ta gane kuskurenta."
Abdullahi ya ce APC ba ta da ikon magana kan PDP har sai ta cika shekaru 16 a kan mulki kamar yadda PDP ta yi a baya.
Atiku ya ce Tinubu ya lalata nasarar 12 ga Yuni
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce gwamnati mai ci ta lalata duk wani cigaba da aka samu daga gwagwarmayar 12 ga Yuni, yana mai cewa:
“Wadanda suka sadaukar da rayuwarsu ba su yi hakan ba domin ‘yan Najeriya su ci gaba da wahala.”
Punch ta rahoto cewa Atiku ya ce jam’iyyun adawa na ci gaba da shirya haɗin gwiwa don kare abin da gwagwarmayar 12 ga Yuni ke wakilta.

Asali: Facebook
SDP da Obi su ma sun yi martani ga Tinubu
Jam’iyyar SDP ta ce furucin Tinubu “rashin ƙwarewa ne a shugabanci” kamar yadda kakakin jam’iyyar, Araba Aiyenigba, ya bayyana.
Shi ma kakakin yakin neman zaben Obi-Datti, Dr. Yunusa Tanko, ya ce Tinubu ya tabbatar da zargin Obi na cewa gwamnatin APC ce ke da hannu wajen jefa jam’iyyun adawa cikin rikici.
Tinubu ya musanya zargin kafa jam'iyya 1 a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya musa cewa yana shirin mayar da Najeriya karkashin jam'iyya daya.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin da ya yi jawabin ranar dimokuradiyya a zauren majalisar tarayya a Abuja.
A yayin jawabin nasa, Bola Tinubu ya ce Najeriya na kan turba madaidaiciya saboda kokarin da majalisa ta yi a shekarun baya.
Asali: Legit.ng