Tinubu: "Ina Jin Dadin Ganin Jam'iyyun Adawa a Wargaje"

Tinubu: "Ina Jin Dadin Ganin Jam'iyyun Adawa a Wargaje"

  • Shugaban ƙasa ya jaddada cewa Najeriya ba za ta koma tafarkin jam’iyya ɗaya ba, domin hakan saba wa dimokuraɗiyya ne
  • Tinubu ya ce amma duk da haka, jam’iyyarsu za ta ci gaba da karɓar ’yan adawa da ke sha’awar sauya sheƙa zuwa APC
  • Shugaban ya bayyana cewa yana jin daɗin rikicin cikin gida da ke addabar ’yan adawa, yana mai cewa ba nauyinsa ba ne a gyara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai karya dimokuraɗiyya ta hanyar mayar da Najeriya kan tafarkin jam’iyya ɗaya ba.

Ya bayyana hakan ne yayin jawabin ranar Dimokuraɗiyya da ake gudanarwa a yanzu haka a gaban Majalisar Dokokin Ƙasa.

Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Najeriya
Tinubu ya fadawa yan adawa magana Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cikin jawabin da majalisar ta yada kai tsaye a shafinta na Facebook, Tinubu ya ce Najeriya ba ta shirya zama ƙasa mai tafiya a tsarin jam’iyya ɗaya ba.

Tinubu: "Ba za a rufe ƙofar APC ba"

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce jam’iyyarsu ta APC ba za ta rufe ƙofarta ba ga ’yan adawa da ke da sha’awar shiga tafiyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa duk da ba shi da niyyar tilasta tafarkin jam’iyya ɗaya, hakan ba yana nufin cewa APC ta daina karɓar ’yan adawa ba.

Tinubu ya yi jawabi ranar dimokuraɗiyya
Tinubu ya ce ba hakkinsa ba ne daidaita jam'iyyun adawa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Tinubu ya kuma yi maraba da wasu jiga-jigan ’yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom da Francis Oborevwori na jihar Delta.

Haka kuma ya kafa da yiwa dukkanin yan siyasar da suka sauya sheka zuwa APC maraba, tare da cewa sun shigo tafiya mai kyau.

Tinubu ya jefawa ’yan adawa magana

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa yana jin daɗin yadda jam’iyyun adawa suka shiga cikin rikici da rarrabuwar kai, yana mai cewa ba aikinsa ba ne ya gyara musu jam’iyya.

A cewarsa:

"Ina jin dadin ganin yan adawa a hargitse."

Ya ƙara da cewa ƙofar APC a bude take ga duk wani ɗan adawa da ke son shiga jam’iyyar, inda ya ce abu mafi kyau shi ne a rungumi yan adawa dake sauya sheka.

Tinubu na wannan batu ne a lokacin da ake zargin APC da amfani da karfin gwamnati wajen murkushe yan adawa.

An roki Tinubu ya maido Fubara kujerarsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Cif Bode George, ya roƙi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya maido da Siminalayi Fubara kujerarsa ta gwamnan jihar Ribas.

Bode George, wanda jigo ne a jam'iyyar PDP ya ce dawo da Fubara mukaminsa zai yi ma'ana a wani bangare na bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana da ake yi a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa tun da Tinubu zai iya yafewa gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu, kamata ya yi ya yafewa Siminalayi Fubara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.