Tinubu Ya Tafka Kuskure a Jawabin Ranar Dimokuradiyya, Gwamnati Ta ba da Hakuri
- Shugaba Bola Tinubu ya lissafa sunayen mutane biyu da ke raye a cikin jerin matattun da aka karrama a jawabin Ranar Dimokuraɗiyya
- Fadar shugaban ƙasa ta bakin Bayo Onanuga ta fitar da sanarwar neman afuwar jama'a, tana mai cewa ba ayi kuskuren da gangan ba
- An tabbatar da cewa za a gyara sunayen da aka bayar a shafukan gwamnati, yayin da aka jaddada girmamawa ga waɗanda aka ambata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta fito ta ba da haƙuri bayan wani babban kuskure da aka samu a jawabin Shugaba Bola Tinubu na ranar Dimokuraɗiyya.
A cikin jawabinsa, Tinubu ya lissafa sunayen fitattun mutane biyu; Pa Reuben Fasoranti da Dr. Edwin Madunagu, cikin jerin matattun da aka karrama, alhalin suna raye.

Asali: Facebook
Gwamnati ta gano kuskure a jawabin Bola Tinubu
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya yi saurin fitar da sanarwar ba da hakurin a yammacin Alhamis, kamar yadda rahoton NTA News ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kuskure, wanda aka watsa kai tsaye a lokacin jawabin shugaban ƙasar na ranar dimokuraɗiyya a majalisar tarayya, ya haifar da rudani da rashin jin daɗi a tsakanin jama'a.
Shugaba Tinubu ya karrama 'yan mazan jiya da manyan jiga-jigan ƙasa saboda gudummawarsu ga dorewar dimokuraɗiyyar ƙasar.
An ba da hakuri kan karrama rayayyu a jerin matattu
A cikin sanarwa da Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin tarayya ta amince da kuskuren kuma ta bayyana shi a matsayin "kuskuren da aka yi ba da gangan ba."
"A ƙarƙashin rukunin lambar yabo ta wadanda suka mutu, an haɗa da sunayen Pa Reuben Fasoranti, shugaban Afenifere, da Dr. Edwin Madunagu, wanda hakan ba daidai ba ne.
"Duk waɗannan fitattun mutane biyu suna nan da ransu, don haka, bai kamata a ga sunayensu a cikin rukunin wadanda aka karrama da suka rasu ba."
- Bayo Onanuga.
Onanuga ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a yi gyare-gyare nan take a dukkanin shafukan fadar shugaban kasa da kuma kafofin yaɗa labarai na jama'a.
SaharaReporters ta rahoto Onanuga ya ƙara da cewa:
"Muna matuƙar nadamar wannan kuskuren. Za mu yi gyare-gyare da suka wajaba a duk shafukan watsa labarai na fadar gwamnatin tarayya."

Asali: Twitter
Tinubu ya karrama sama da mutum 72
An saba gabatar da jawabin ranar dimokuraɗiyya, wanda ke mayar da hankali kan dawowar Najeriya ga mulkin farar hula a ranar 12 ga Yuni, 1999.
Kuma ya zama kamar al'adar shugaban kasa na amfani da ranar bikin dimokuradiyya don karrama jaruman da suka taka rawa wajen kafuwar dimokuraɗiyyar, rayayyu da matattu.
Sai dai bikin wannan shekarar ya kasance mai muhimmanci musamman domin ya kunshi dogon jerin sunayen sama da mutum 72 da suka yi gwagwarmayar dimokuraɗiyya da aka karrama.
An ce Pa Fasoranti (98), shugaban ƙungiyar Yarbawa, da Dr. Madunagu (78), masanin ilimin akidar Markisanci kuma ɗan jarida, suna ci gaba da ba da gudunmawa ga ci gaban kasa.
An karrama Uba Sani, Shehu Sani da wasu 70
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaba Bola Tinubu ya karrama fitattun 'yan Najeriya, ciki har da Gwamna Uba Sani da Shehu Sani, da lambobin yabo a ranar dimokuraɗiyya.
Tinubu ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya maida ranar 12 ga Yuni matsayin Ranar Dimokuraɗiyya, tare da amincewa da nasarar MKO Abiola a zaɓen 1993.
An kuma karrama jarumai da dama da suka sadaukar da rayukansu wajen gwagwarmayar dimokuraɗiyya, ciki har da Kudirat Abiola da Pa Alfred Rewane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng