'Ni Kadai Gayya': Yadda Tinubu Ya Rusa Shirin PDP na Yin Mulki har Abada a 2003
- Shugaba Bola Tinubu ya nesanta kansa da APC daga zargin kafa gwamnatin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa fargabar 'yan adawa ce kawai
- Ya tuna yadda shi kaɗai ya tsaya tsayin daka a 2003 ya ruguza shirin PDP na murkushe 'yan adawa don ta yi mulki na har abada
- Tinubu ya yi maraba da masu sauya sheka zuwa APC, tare da shawartar jam'iyyun adawa da su gyara matsalolinsu maimakon zargin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nesanta kansa da jam’iyyar APC daga zargin cewa suna shirin kafa gwamnatin jam’iyya ɗaya a Najeriya.
Ya bayyana haka ne a jawabinsa na musamman ga taron haɗin gwiwa na majalisar dokoki ta ƙasa, a lokacin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2025.

Asali: Twitter
A jawabinsa, wanda mai taimaka masa kan sababbin kafofin sadarwa, Olusegun Dada ya wallafa a X, Tinubu ya ce waɗannan zarge-zargen sun samo asali ne daga fargabar 'yan adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake jaddada cewa kafa gwamnatin jam'iyya ɗaya a Najeriya ba zai taɓa faruwa ba a ƙarƙashin mulkinsa, Shugaba Tinubu ya ce:
“Ga waɗanda ke hura wutar cewa APC na ƙoƙarin kafa gwamnatin jam’iyya ɗaya a Najeriya, ina ba su tabbacin hakan ba za ta faru ba. Wannan zargin nasu da ya samo asali daga tsoro, ba gaskiya ba ne."
Tinubu ya tuna da gwagwarmayar siyasarsa
Shugaban ƙasar ya yi waiwaye kan tarihin siyasar sa, inda ya ce a shekarar 2003, lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki a wancan lokacin, ta yi ƙoƙarin murkushe ‘yan adawa.
Tinubu ya ce shi kaɗai ne gwamnan da ya tsaya kyam kan kishin kare dimokuraɗiyya a yankinsa, tare da kin amincewa PDP ta kafa gwamnatin jam'iyya ɗaya.
“Sun ce za su yi mulkin Najeriya na tsawon ƙarnoni. Amma ina suke yanzu? Ni ɗaya na zama gayya, na tsaya kyam. Amma duk da ƙarfin su, ba su iya sarrafa ƙaddarar Ubangiji ba, domin bakin alƙalami ya riga ya bushe."
- Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce wannan yunƙuri da aka yi wancan lokacin na kafa jam’iyya ɗaya ne ya haifar da yunƙurin haɗakar ‘yan adawa wanda daga bisani ya haifar da kafa jam’iyyar APC.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa:
“Ba zan maimaita kuskuren siyasa na wancan lokacin ba. Kafa jam’iyya ɗaya ba zai faru ba – kuma bai kamata ya faru ba."
Sauya sheƙa: “A gyara gida kafin a zargi wasu”
Tinubu ya tabo batun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC da ya faru a ‘yan kwanakin nan, musamman daga jihohin Delta da Akwa Ibom.
Ya yi maraba da sababbin ‘yan jam’iyyar kamar Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta da Pastor Umo Eno na Akwa Ibom, da wasu mambobin majalisa.
“Zai zama babban kuskure a siyasance idan muka rufe ƙofar shiga jam’iyyar APC ga waɗanda ke sha’awar sauya sheƙa zuwa gare mu."
- Shugaba Bola Tinubu.
Ya shawarci sauran jam’iyyun siyasa da su mayar da hankali wajen gyara gidajensu, maimakon zargin APC da abinda ba su da hujja a kai.
Shugaban ƙasar ya ce:
“Ya kamata jam’iyyun da ke fargaba kan sauyin sheƙa su duba halin da jam’iyyarsu ke ciki. Ku gyara gidajenku. Ba zan iya taimaka muku kan hakan ba. Abin jin daɗi ne ma ganin yadda kuke cikin rikici yanzu."

Asali: Twitter
“Gasa tsakanin jam’iyyu alheri ne a dimokuraɗiyya”
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gasa tsakanin jam’iyyu na da amfani ga ci gaban ƙasa. Ya ce Najeriya ba za ta taɓa samun ci gaba ba idan aka kawo ƙarshen ‘yan adawa.
“Dole mu karɓi bambancin jam’iyyu kamar yadda muke karɓar bambancin jama’ar ƙasa. Ba ma buƙatar kawar da ‘yan adawa, sai dai mu tabbatar da cewa gasar siyasa tana amfani ga al’umma."
- Shugaba Bola Tinubu.
Ya kammala da kiran hadin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisa, da kuma tsakanin jam’iyyun siyasa daban-daban, don magance kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da ƙasar ke fuskanta.
Karanta cikakken jawabin Tinubu a nan kasa:
Tinubu ya karrama fitattun 'yan Najeriya 72
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya karrama fitattun 'yan Najeriya 72, ciki har da marigayi Shehu Musa Yar'Adua, saboda gudummawarsu ga dimokuraɗiyya.
Tinubu ya jinjinawa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari bisa maida 12 ga Yuni matsayin Ranar Dimokuraɗiyya da amincewa da nasarar MKO Abiola a zaɓen 1993.
An karrama jarumai da dama da suka sadaukar da rayukansu wajen gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya, ciki har da Kudirat Abiola da Sanata Shehu Sani.
Asali: Legit.ng