"Wa Ya Samu Nasara?": Ana Zargin An Rubuta Sakamakon Zaben Shugaban Ƙasa na 2027

"Wa Ya Samu Nasara?": Ana Zargin An Rubuta Sakamakon Zaben Shugaban Ƙasa na 2027

  • Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar AAC a 2023, Omoyele Sowore ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ƙarisa kashe Najeriya
  • Sowore ya caccaki tsarin gwamnatin Bola Tinubu, yana mai zargin cewa an riga an rubuta sakamakon babban zaɓen 2027
  • Ɗan gwagwarmayar ya ce ba zai iya haɗa kai da LP ko Peter Obi ba saboda su mutane ne ba su san komai ba sai kansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Omoyele Sowore, ɗaya daga cikin fitattun masu adawa a Najeriya, ya bayyana ra’ayinsa game da mulkin Shugaba Bola Tinubu, kassara adawa, da sauran batutuwan siyasa.

Tsohon ɗan takarar shugaban kasar ya ce tun a baya, ya yi hasashen cewa ƴan Najeriya za su sha wahala a mulkin Tinubu ta yadda sai sun ji kamar Muhammadu Buhari ya dawo.

Omoyele Sawore
Sawore ya caccaki salon mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OmoyeleSawore4
Asali: Twitter

Sowore ya yi ikirarin cewa Tinubu ya yi mummunan barna a fanonin tattalin arziki, siyasa da ilimi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sowore ya caccaki salon mulkin Tinubu

"Buhari ya kashe Najeriya cikin shekaru takwas, Tinubu kuma yana binne ta cikin shekara biyu.”

Omoyele Sowore ya ce Tinubu ya kori gaskiya daga gwamnati kuma yana mulki da danniya maimakon dimokuraɗiyya.

Sowore ya soki kudirin da ke gaban Majalisar Tarayya wanda ke son a tilasta wa duk ɗan Najeriyar da ya kai munzali fita ya kaɗa ƙuri'a.

“Idan har za a yi barazana domin tilasta mutane yin zaɓe, to dimokuraɗiyya ta mutu. Mutane ba za su amince da tsarin da ba zai ba su damar zaɓen wanda suke so ba."

Ana zargin an rubuta sakamakon zaɓen 2027

Game da batun sauya shekar da ake ta yi zuwa APC, Sowore ya ce:

“Babu adawa ta gaskiya, yawancin waɗanda ke canza jam’iyya ba su da akida. Ba wai suna neman canji bane, suna sauya sheka ne don shiga jirgin da za a raba ganima.

Sawore da Bola Tinubu.
Sawore ya yi zargin cewa an gama rubuta sakamakon zaben 2027 Hoto: @OmoyeleSawore, @aonanuga1956
Asali: Twitter

Bugu ɗa ƙari, Sowore ya ce ba zai shiga haɗaka da Peter Obi ko LP ba, yana mai cewa sun fi mayar da hankali kan kamfen ɗin 'yes daddy' da son kansu kaɗai.

Game da yiwuwar tsayawa takara a 2027, Sowore ya ce:

“Ba zan taɓa daina fafutuka ba, ko a kotu, ko a zanga-zanga, ko a filin siyasa. Amma game da zaɓe? Ban yarda da tsarin zaɓen yanzu ba, ina tunanin sun riga sun rubuta sakamakon zaɓen 2027.

Duk da nauyin wannan magana, Sowore bai kawo hujjar cewa an yi magudi ko kuwa za a murde zabe mai zuwa ba.

Peter Obi ya yi magana kan haɗaka

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ya ce ba kowane ƙawancen adawa zai shiga ba.

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce zai shiga kawance ne kaɗai idan ya kasance manufarsa yaƙi da mulkin zalunci, yunwa da fatara.

A cewarsa, haɗakar da yake ta banbanta da wacce ake magana domin manufarsa kawo karshen mulkin zalunci, yayewa jama'a yunwa da talauci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262