"Tinubu Ya Dage sai an Magance Matsalar Tsaro a 2025," Badaru Ya Faɗi Halin da Ake ciki

"Tinubu Ya Dage sai an Magance Matsalar Tsaro a 2025," Badaru Ya Faɗi Halin da Ake ciki

  • Ministan Tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya matsa ƙaimi sai an magance matsalar tsaro a 2025
  • Badaru ya bayyana cewa an samu nasara mai girma a ƙoƙarin kakkaɓe duka ƙalubalen tsaron da ake fama da su a sassan Najeriya
  • A cewar ministan, shugaban ƙasa Tinubu bai taɓa kin amincewa da buƙatar da aka kai masa game da sayo kayan aiki ga sojoji ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Najeriya na samun gagarumar nasara a yaƙi da ƴan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro.

Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce alamu sun nuna an samu sauƙin matsalar tsaron da aka kwashe shekaru ana fama da ita a ƙasar nan.

Badaru Abubakar.
Badaru ya ce Shugaba Tinubu ya bada umarnin dawo da zaman lafiya a 2025 Hoto: Muhammad Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi shi yayin da ake shirye-shiryen bikin cikar Shugaba Tinubu shekara biyu a kan mulki, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zaman lafiya ya fara dawowa" - Badaru

Badaru ya ce:

"A karon farko cikin shekaru, yanzu mutane na iya tafiya daga Birnin Gwari zuwa Kaduna ko da tsakar dare ne.
"Haka ma hanyar Zaria zuwa Funtua zuwa Gusau yanzu an samu zaman lafiya, ga kuma hanyar Abuja-Kaduna.”

Wane umarni Tinubu ya bayar kan tsaro?

Badaru ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya bai wa jami’an tsaro umarni kai tsaye da su kawo ƙarshen matsalolin tsaro kafin ƙarshen shekara ta 2025.

Ya jaddada cewa ayyukan soji kamar Operation Fasan Yama da sauran hare-haren da ake kaiwa a sassa daban-daban sun taimaka matuƙa wajen dawo da zaman lafiya.

Tsaro: Nasarorin da aka samu a mulkin Tinubu

A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, an samu manyan nasarori da suka haɗa da:

  • Kashe ƴan ta'adda 13,543
  • Kama ƴan ta'adda 17,500
  • Ceto mutane 9,821 da aka sace
  • Ƴan ta'adda 24,000 sun miƙa wuya

“Wadannan ba kawai lissafi ba ne, rayuka ne da aka ceto daga kangin wahala, kuma aka kwato garuruwa, sannan aka mai da jama'a gidajensu," in ji Badaru.

Ya ce harkokin kasuwanni da gonaki sun fara dawowa a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, kamar yadda PM News ta kawo.

Shugaba Tinubu.
Badaru ya bayyana gagarumar nasarar da aka samu a yaƙi da ƴan ta'adda Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya inganta walwalar sojoji

Badaru ya kuma bayyana cewa Tinubu ya ware Naira biliyan 18 domin biyan basussukan inshora na sojoji da kuma ƙarin kuɗin abinci daga ₦1,500 zuwa ₦3,000 ga kowanne soja a kullum.

“Shugaban ƙasa bai taɓa watsi da bukatar sayo kayan aiko ba, da an kai masa yake amincewa. Yanzu muna da jiragen yaƙi ƙirar, UAVs, MRAPs, APCs da kayan yaƙi na zamani.”

Game da tattalin arziki, Badaru ya ce an samu raguwar fasa bututun mai da satar man fetur a yankin Niger Delta, ɗanyen man da ake samarwa ya ƙaru daga ganga miliyan 1.4 zuwa kusan ganga miliyan 1.8 a rana.

Tinubu ya kaddamar da sababbin jiragen yaƙi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da sababbin jiragen helikwafta da ya sayo wa dakarun rundunar sojin saman Najeriya.

An samar da jiragen helikwafta biyu, NAF544 da NAF545, ne domin karfafa karfin rundunar sojin sama wajen yaki da matsalolin tsaro.

Hafsun Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa rundunar za ta karbi karin jirage 49 nan da shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262