Peter Obi Ya Kara Jefa Mutane a Duhu, Ya Yi Magana kan Shirin Kayar da Tinubu a 2027

Peter Obi Ya Kara Jefa Mutane a Duhu, Ya Yi Magana kan Shirin Kayar da Tinubu a 2027

  • Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya bayyana cewa yana cikin tawagar ƴan adawa da za su ƙulla kawance gabanin zaɓen 2027
  • Sai dai Mista Obi ya ce ya haɗakar da yake ciki manufarta shi ne shugabanci mara kyau da yaƙi da talauci da yunwa a ƙasar nan
  • Wannan kalamai na zuwa ne a lokacin da wani rahoto ya bayyana cewa Atiku ya yi wa Obi tayin takarar mataimakin shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya jaddada cewa yana cikin waɗanda za su haɗa ƙawance domin yaƙar gurɓataccen shugabanci.

Mista Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra ya ce haɗakar da yake ciki za ta yaƙi shugabanci na zalunci, yunwa da talaucin da suka addabi ƴan Najeriya.

Peter Obi.
Peter Obi ya tabbatar da cewa yana cikin ƴan adawar da ke shirin haɗewa wuri ɗaya kafin 2027 Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

Obi ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake amsa tambaya daga jaridar Vanguard kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya cimma yarjejeniya da Atiku Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Atiku ya yi wa Peter Obi tayin mataimaki

Rahoton da ke yawo a kafafen watsa labarai ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi wa Obi tayin takarar mataimakin shugaban kasa a 2027.

Bayan haka kuma, rahoton ya yi ikirarin cewa Atiku ya yi alƙawarin yin zango ɗaya kaɗai idan suka samu nasara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Wannan jita-jita dai ta ja hankalin ƴan Najeriya, wadanda suka jima suna dakon ganin wane shiri ƴan adawa suke yi na kawar da APC a zaɓen 2027.

Atiku ya cimma yarjejeniya da Peter Obi?

Da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a Kubwa, inda ya bada gudummawa don gina makaranta da asibiti da cocin Anglican ta shirya, Obi ya ce yana cikin haɗaka amma ta yaƙi da yunwa da talauci.

A cewarsa, haɗakatr da yake ta banbanta da wacce ake magana domin manufarsa kawo karshen mulkin zalunci, yayewa jama'a yunwa da talauci.

Obi, Atiku da Tinubu.
Peter Obi ya faɗi manufar ƙulla kawancen ƴan adawa gabanin 2027 Hoto: Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me yasa Obi ya shiga haɗakar ƴan adawa?

A rahoton da Channels tv ta wallafa yau Litinin, Peter Obi ya ce

"Za ku iya fassara rahoton yadda kuke so, amma ni ina cikin hadaka ne domin yaki da gurɓataccen shugabanci, yunwa da talauci."

Peter Obi bai musanta raɗe-raɗin cewa zai yi takara da Atiku ba kai tsaye, haka kuma bai tabbatar da cewa yana cikin tawagar ƴan adawa da ke shirin haɗaka gabanin 2027 ba.

Atiku ya jero jam'iyyun da za su hada-kai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce APC, PDP da LP na cikin waɗanda ke shirin haɗaka gabanin 2027.

Alhaji Atiku ya tabbatar da cewa manyan jiga-jigai daga waɗannan jam'iyyu sun shirya ƙulla kawance domin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

'Dan takarar shugaban kasa a PDP a 2023 ya fadi haka ne yayin da jiga-jigai daga PDP suka kai masa ziyara karkashin jagorancin Simon Achuba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262