Peter Obi Ya Yi Magana kan Zargin Ganawa da Tinubu a Boye kan Bashin N225bn

Peter Obi Ya Yi Magana kan Zargin Ganawa da Tinubu a Boye kan Bashin N225bn

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya fito ya kare kansa kan zargin neman ganawa da Shugaba Bola Tinubu
  • Peter Obi ya bayyana ceqa bai taɓa neman ganawa da shugaban ƙasan ba kan bashin N225bn da ake zargin an biyo bankin Fidelity
  • Shahararren d an siyasan ya bayyana cewa masu yaɗa jita-jitar ba abin da suka tasa a gaba sai ƙoƙarin ganin sun ɓata masa suna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya yi martani kan zargin cewa ya je birnin Rome ne domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Peter Obi ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya je ne domin ganawa Shugaba Tinubu kan bashin N225bn da aka ce yana da alaƙa da bankin Fidelity.

Peter Obi, Bola Tinubu
Peter Obi ya musanta ganawa da Tinubu kan bashin bankin Fidelity Hoto: @PeterObi/@officialABAT/@fidelitybankplc
Asali: Twitter

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rahoto daga wata kafar yaɗa labarai ya zargi Peter Obi da cewa ya yi wata ɓoyayyar ganawa da Tinubu a birnin Rome domin neman shiga tsakani kan badaƙalar kuɗi da ta shafi bankin Fidelity.

Peter Obi ya musanta ganawa da Tinubu

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya nesanta kansa da wannan zargi, yana mai cewa bai taɓa neman ganin shugaba Tinubu ba, balle ya yi magana da shi dangane da wani banki.

Peter Obi ya bayyana cewa rahoton wani ɓangare ne na ƙoƙarin ɓatanci da ɓata masa suna.

"A bayyane yake cewa mafi girman kasuwancin masu ɓatanci a yanzu shi ne yin magana kan Peter Obi daga kowace fuskar ƙarya da mummunan ra’ayi."
"Hatta tafiyata mai tsarki zuwa Rome, da nufin bauta da ibada, an karkatar da ita zuwa wani sabon salon ɓatanci daga hannun waɗanda ake biyansu domin yaɗa duk wani abu mara kyau game da Peter Obi."

“Ban taɓa neman ganawa da Shugaba Tinubu ba, kuma ban taɓa ganawa da shi tun da ya hau mulki ba, sai dai minti ɗaya kacal da muka haɗu a harabar cocin Saint Peter’s Basilica a Rome yayin taron ƙaddamar da Paparoma Leo XIV, inda na gaishe shi da sauran manyan baƙi a wurin cikin girmamawa.”

- Peter Obi

Menene alaƙar Peter Obi da bankin Fidelity?

Peter Obi ya kuma fayyace alaƙarsa da bankin Fidelity, yana mai cewa ba shi ne mai bankin ba.

Peter Obi
Peter Obi ya ce ba shi ba ne mamallakin bankin Fidelity Hoto: @PeterObi/@fidelitybankplc
Asali: Twitter
“Wanda ke kiran kansa shugaban masu ɓatanci da waɗanda ke cin moriyar yaɗa ƙarya da cutar da mutane, sun kuma yi ƙarya da cewa ni ne mai bankin Fidelity. Don fayyace gaskiya, ba ni ne mamallakin bankin ba."

- Peter Obi

Ministan Tinubu ya ba Peter Obi shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan ayyuka a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya ba Peter Obi shawara.

Dave Umahi ya buƙaci tsohon gwamnan na jihar Anambra da ya goyawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya

Ministan ya shawarwaci Peter Obi da ya haɗa kai da sauran shugabannin yankin Kudu maso Gabas wajen nuna goyon baya ga Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng