2027: An Samu Wanda Zai Buga da Tinubu, Jigo Zai Fito Takarar Shugaban Ƙasa a APC

2027: An Samu Wanda Zai Buga da Tinubu, Jigo Zai Fito Takarar Shugaban Ƙasa a APC

  • Cif Charles Udeogaranya ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2027
  • Jigon ya yi watsi da matsayar da shugabannin APC suka cimma ta ba Shugaba Bola Tinubu tikitin kai tsaye babu hamayya
  • Ya ce babu zancen fitar da ɗan takara ta hanyar masalaha a APC a daidai lokacin da yunwa da fatara suka yi katutu a kasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar APC a 2019, Cif Charles Udeogaranya, ya sake dawowa da nufin takara a zaɓen 2027.

Jigon APC ya yi watsi da matakin da jam'iyyar ta ɗauka na bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tikitin tazarce ba tare da hamayya ba.

Shugaba Tinubu.
Jigon APC zai kara da Tinubu wajen neman tikitin takarar shugaban kasa na APC a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Udeogaranya ya yi fatali da wannan matakin, ya ce babu batun nuna fifiko da ƙarfa-ƙarfa a tsarin dimukuraɗiyya, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan siyasar ya yi wannan furuci ne bayan goyon bayan da shugabannin APC, gwamnoni da 'yan majalisar dokoki suka bai wa Shugaba Bola Tinubu a Taron Koli na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.

APC ta samu ɗan takarar da zai kara da Tinubu

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Udeogaranya ya ce:

“Babu wata doka a tsarinmu da ta tanadi bayar da tikiti kai tsaye babu hamayya ga wani ɗan takara. Zan tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a 2027.”

Jigon jam'iyya mai mulki ya kara da cewa babu zancen fitar da ɗan takara ta masalaha ko a ce kowa ya aminta da shi a irin wannan halin da ƙasar nan take ciki, rahoton Daily Post.

Najeriya na buƙatar canjin shugabanci

Cif Udeogaranya ya koka cewa ƴan Najeriya na cikin halin talauci, yunwa da rashin tsaro wanda ya haifar da fargaba, yana mai cewa akwai buƙatar a samu canji.

“Babu zancen masalaha kan yunwa da fatara, babu wata masalaha kan matsalolin tattalin arziki, babu kan rashin tsaro, babu wata masalaha dole mu tashi mu ceto ƙasar mu.
"Ba za mu ba tsarin dimukuraɗiyya kunya ba a 2027, ba wanda zai hana ni takara, zan fito domin doka ta bani ƴanci," in ji shi.
Bola Tinubu da Udeogaranya.
Jigon APC ya ce zai fafata da Tinubu wajen neman tikitin APC a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Chief Charles Udeogaranya
Asali: Facebook

Udeogaranya ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasa domin gina sabuwar Najeriya da za ta dogara da ƙirƙira, kishin ƙasa da samar da walwala ga ƴan ƙasa.

Ya ƙara da cewa akwai bukatar kafa sabon shugabanci mai gaskiya da hangen nesa, ba dogaro da amincewar jam’iyya kawai ko muradin wasu mutane ba.

Yahaya Bello zai nemi takara a 2027?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya tabbatar da cewa zai nemi takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.

Alhaji Yahaya Bello ya ce ba yadda za a yi ya kara da mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai nesanta kansa da bidiyon da ake yaɗawa.

Tsohon gwamnan ya ce yana tare ɗa Shugaba Tinubu kuma zai mara masa baya domin ya yi tazarce a zaɓe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262