Dan Shekara 45 Ya Fada Tsohuwar Rijiya Yana Kokarin Ciro Waya, Ya Mutu har Lahira

Dan Shekara 45 Ya Fada Tsohuwar Rijiya Yana Kokarin Ciro Waya, Ya Mutu har Lahira

  • Wani mutum mai shekaru 45, mai suna Yusuf Usman, ya rasu bayan ya fada wata tsohuwar rijiya a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano
  • Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kuma hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar sa a cikin wata sanarwa da ta ya fitar
  • A cewar sanarwar, hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:13 na safe daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta mai suna Kabiru Tata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani mutum mai shekaru 45, Yusuf Usman, ya rasu bayan ya faɗa cikin tsohuwar rijiya yayin da yake ƙoƙarin ɗauko wayar salula a garin Kwa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar a jihar Kano, Saminu Abdullahi ya bayyana cewa an yi kokarin ceto da rai amma ƙaddara ta riga fata.

Kara karanta wannan

Za a yi auren gata a Kano, 'yan mata, zawarawa da samari 3,000 za su angwance

Ana kokarin ceto wanda ya fada rijiya a Kano
Jami'an kashe gobara na kokarin ceto wanda ya fada rijiya a Kano. Hoto: Saminu Yusif
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce sashen agajin gaggawa na hukumar ya samu kira domin a ceto mutumin da misalin karfe 11:13 na safiyar Laraba.

Mutum ya mutu a rijiya saboda waya

Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce an tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar zuwa wurin da mutumin ya fada rijiya nan take.

“Da isar tawagar ceto wurin, sun tarar da mutumin ya makale a cikin rijiyar da aka mayar wurin zubar da shara. An samu nasarar ceto shi alhali ya suma, amma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa, wanda ake zargin ya samo asali ne daga ƙarancin iska da kuma tsananin zafi a cikin rijiyar,”

In ji Abdullahi a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Yadda aka yi da gawar mutumin

Hukumar kashe gobara ta bayyana cewa an miƙa gawar mamacin ga mai unguwar Kwa, Alhaji Muktar, domin shirya jana’izarsa bisa koyarwar Musulunci.

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

Jama'a da dama sun masa addu'o'i fatan samun rahamar Allah tare da fatan Ubangiji ya kiyaye faruwar irin haka a nan gaba a yankin.

Gargadin hukumar kashe gobara

Abdullahi ya kuma bayyana cewa shugaban hukumar kashe gobara, Alhaji Sani Anas, ya buƙaci al’umma su tabbatar da cewa an rufe rijiyoyi yadda ya kamata.

Shugaban hukumar ya bukaci a rika cike dukkan rijiyoyin da aka daina amfani da su domin kauce wa irin wannan mummunan lamari a gaba.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Haka kuma ya yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su ɗauki matakan kariya domin tabbatar da tsaron muhalli da kare rayukan jama’a.

Babban dan kasuwa a Kano ya rasu

A wani labarin, mun kawo muku cewa fitaccen ɗan kasuwar mai kuma mai harkar gidaje a Kano, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager, ya rasu yana da shekaru 68.

Ɗansa, Surajo Audu Manager, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce ɗan kasuwar ya rasu ne da safiyar Laraba a Asibitin Saudi German da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Allah ya karbi rayuwar Audu Manager ne bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng