'Ku Bi Ni ko Ku Yi Murabus': Gwamnan PDP Ya Kammala Shirinsa na Komawa APC
- Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya bukaci kwamishinoni da masu mukami su koma APC tare da shi ko su yi murabus daga mukamansu
- A wani taron majalisar zartarwa, Eno ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP saboda yana goyon bayan salon shugabancin Bola Tinubu
- Ya gargadi masu mukami da kada su yi tunanin za su yi amfani da PDP don kalubalantar sa, yana mai cewa shi zai rike jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya yi magana kan shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki.
Gwamnan ya ba muƙarrabansa shawarwari kan makomarsu bayan kama hanyar ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC a Najeriya.

Asali: Twitter
Gwamna Eno ya yi magana ne a wani taron majalisar zartarwa da ake yi a ranar Alhamis 22 ga watan Mayun 2025, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gwamna Eno ke kwadayin komawa APC
Gwamnan na daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa da ya fito ƙarara yake bayyana shirinsa na komawa APC mai mulkin Najeriya.
Eno ya sha bayyana haka a wuraren taruka tare da nuna goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Tinubu game da zaben 2027 da ke tafe.
Hakan bai rasa nasaba da komawar Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta da ya yi ta maza ya koma APC tun da wuri.

Asali: Twitter
Umarnin da Gwamna Eno ya ba muƙarrabansa
Gwamnan ya umarci dukkan kwamishinoni da masu mukami a gwamnatinsa su koma APC ko su yi murabus, The Guardian ta ruwaito.
Majiyoyi daga taron sun ce Gwamna Eno ya bayyana cewa:
“Duk wanda ya ce bai san niyyata ta barin PDP ba, yana rayuwa ne a karni na 18.”
Ya bayyana cewa sha’awar salon shugabancin Shugaba Bola Tinubu ne ya sa shi yanke shawarar yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya.
Wadanda gwamna zai so su bi shi APC
Gwamnan ya fadi karara cewa bai da abin tattaunawa da wanda bai yarda da tunaninsa ba, sai zababbun ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi.
Ya kara da cewa:
“Duk wanda ke tunanin zai yi amfani da PDP don ya kalubalance ni bayan na fice, yana yaudaran kansa, domin zan ci gaba da rike jam’iyyar.”
A lokacin da ake hada wannan rahoto, har yanzu taron majalisar zartarwa yana gudana, inda ake sa ran sabbin bayanai za su bayyana nan gaba.
Gwamna ya magantu kan shirin barin PDP
A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sake nuna alamun zai fice daga jam'iyyar PDP gabanin babban zaɓen 2027.
Gwamna Eno ya ce a halin yanzun bai san wace jam'iyya zai koma ba a nan gaba, amma ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai yi wa kowa adalci.
Umo Eno ya nanata cewa shi gwamna ne na kowane dan Akwa Ibom ba tare da la'akari da jam'iyyun siyasa ba inda ya shawarci yan jihar kan hakuri da lamarin gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng