Ana tsakiyar Taron Ƙusoshin APC, Akpabio Ya Kawo Batun Tsige Shugaba Tinubu
- Sanata Godwill Akpabio ya yi magana kan aikawa Shugaba Bola Tinubu takardar sanarwar tsigewa, yayin taron koli na jam'iyyar APC
- Shugaban majalisar dattawan ya ce majalisa ba ta yi yunkurin tsige Shugaba Tinubu ba saboda yana tafiyar da kasar yadda ya kamata
- Ya jaddada cewa duk da matsin tattalin arziki, Tinubu ya dora Najeriya kan tafarkin ci gaba, don haka suka ga dacewar ya zarce a 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugabannin majalisar dattawa da ta wakilai sun bayyana cikakken goyon bayansu ga muradin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin tazarce a 2027.
Shugaban sanatoci, Godswill Akpabio, ne ya gabatar da wannan kudiri a ranar Alhamis yayin taron kolin jam’iyyar APC da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Facebook
Akpabio ya kawo batun tsige Shugaba Tinubu
A cewar jaridar Punch, Akpabio ya amince cewa Tinubu ya fuskanci kalubale a zaben 2023, amma ya nuna kwarin guiwa cewa a 2027, jam’iyyar APC za ta karbe karin jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar ya ce:
“Idan wannan shugaban ya yi aiki nagari, ba nauyinmu ba ne mu yaba masa? Kuma idan bai yi aiki nagari ba, ba hakkinmu ne mu aika masa da sanarwar tsige shi ba?
“Ba mu aika masa da sanarwar tsige wa ba, mun fada masa cewa 2023 ta jijjiga shi sosai. Amma a 2027, abubuwa za su canza. Za a samu karin jihohi masu goya masa baya.”
Akpabio, tare da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, sun bayyana cikakken goyon baya ga Tinubu.
Akpabio ya amince Tinubu ya yi tazarce
Ya ƙara da cewa duk da matsalolin tattalin arziki da kasa ke fuskanta, Shugaba Tinubu yana aiki tukuru domin farfado da Najeriya.
“Duk da wahalhalun da ake fama da su, ya dora Najeriya a kan hanyar ci gaba, wanda al’ummomin duniya da kungiyoyi na kasa da kasa suka tabbatar.
“Jama’a musamman talakawa na cike da kwarin gwiwa a kan mulkinsa. Har wasu sanatoci suna cewa ba su taɓa ganin abubuwa sun tafi daidai kamar yanzuba.”
- Godswill Akpabio.
Kafar VON ta rahoto cewa, shugaban majalisar ya kara da cewa:
“Don haka, ina gabatar da kudiri cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kadai ne zai zama dan takarar shugaban kasa na APC a 2027, kuma ya zama zaɓin gama-gari na 'yan Najeriya.”

Asali: UGC
Shugabannin majalisa sun goyi bayan Tinubu
Akpabio ya yi nuni da cewa jam’iyyun adawa musamman PDP sun rude, kuma Tinubu ne ya kamata ya ci gaba da mulki.
“Duk sauran jam’iyyu sun rikice. Na je jihata na ga lemar PDP duk ta huhhuje. Nan ba da jimawa ba za ku ji labari, ko da yake ba za a ji mutuwar sarki a baki na ba.
“Saboda haka, a matsayina na shugaban majalisar dattawan Najeriya, ina gabatar da kudiri cewa Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da mulki; da farko a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, sannan kuma a matsayin shugaban Najeriya a 2027.”
- Godswill Akpabio.
Wannan matsaya ta samu cikakken goyon baya daga shugabannin majalisar tarayya, ba tare da wani ya yi musu ba.
Sanatocin PDP 3 sun mara wa Tinubu baya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dukkanin sanatocin PDP na jihar Osun sun bayyana cikakken goyon bayansu ga kudurin tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Sanatocin sun bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu sun rage tsadar rayuwa, inganta tsaro, tare da amfanar al’ummar da suke kai tsaye.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara tsananta a Osun, bayan hukuncin kotu da ya mayar da shugabannin APC da aka sauke.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng