Lawal Daura Ya Ƙi Amince wa da Zaben ADC a Katsina, Ya Yi Barazanar zuwa Kotu

Lawal Daura Ya Ƙi Amince wa da Zaben ADC a Katsina, Ya Yi Barazanar zuwa Kotu

  • Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura, ya ƙi amincewa da tsarin da ADC ta bi wajen fitar da ɗan takarar gwamna a jihar Katsina
  • Daura ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a takarar gwamna kuma bai amince da batun karbar takarar sanatan Daura ba
  • Ya yi barazanar zuwa kotu idan jam’iyyar ta gaza gudanar da sahihin tsari na sulhu ko zaɓen fitar a gwani cikin gaskiya da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Lawal Daura, ya yi watsi da tsarin da jam’iyyar ADC ta bi wajen fitar da ‘yan takara a jihar Katsina.

Daura ya zama mutum na biyu cikin masu neman tikitin gwamna da ya fito fili yana ƙalubalantar tsarin bayan Mustapha Inuwa ya bayyana cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani ba a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takara a ADC ya fice daga jam'iyyar, ya koma layin Pantami a PDP

Lawal Daura ya ce bai amince da tsarin da ADC ta yi amfani da shi wajen zabar dan takarar gwamna a Katsina ba.
Lawal Daura ya na jawabi a wani taron jam'iyyar ADC a Katsina. Hoto: Lawal Musa Daura
Source: Facebook

Lawal Daura ya dura kan ADC

Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Katsina ranar Lahadi, Daura ya ce rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta cimma matsaya kan ɗan takarar gwamna ta hanyar sulhu ba su da tushe, in ji rahoton Premium Times.

Ya kuma musanta zargin cewa ya amince ya nemi kujerar sanatan Daura maimakon takarar gwamna.

“Tun farko ni takarar gwamna na shiga kuma ban sauya matsaya kan haka ba. Har yanzu ina nan daram a kan burina,” in ji Lawal Daura.

Lawal Daura ya bayyana cewa tsarin da aka bi wajen fitar da ‘yan takara bai yi daidai da dokar zaɓe da kuma ƙa’idojin cikin gida na jam’iyyar ADC ba.

Zarge-zargen Daura kan tsarin ADC

A cewarsa, tun farko masu neman takarar sun jaddada cewa dole ne a bi hanyar sulhu da kowa ya amince da ita ko kuma a gudanar da zaɓen fidda gwani bisa tanadin doka.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ana jita jitar ba malami takara a ADC, Mahadi ya magantu kan janyewa

Lawal Daura ya ce:

“Mun jaddada masu cewa dole ne tsarin ya kasance bisa doka, ko dai ta hanyar sulhu da kowa ya amince da shi ko kuma zaɓen fidda gwani na kato bayan kato. Har yanzu muna jiran a kammala tsarin cikin gaskiya da adalci."

Daura ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da tattaunawa tsakanin masu neman takarar gwamna, yana mai cewa babu cikakken bayani kan yadda aka cimma matsayar da ake ikirari da ita.

“Ana cewa an cimma sulhu, amma babu ɗaya daga cikin masu neman takara biyar da aka yi wa cikakken bayani kan yadda aka kai ga wannan matsaya."

- Lawal Daura.

Daura ya yi barazanar zuwa kotu

Tsohon shugaban DSS ɗin ya bayyana cewa zai iya neman mafita ta shari’a idan jam’iyyar ta gaza bin doka wajen fitar da ɗan takarar gwamna, in ji rahoton jaridar Leadership.

Ya bayyana cewa:

“Idan ba a bi doka ba, ɗaya daga cikin hanyoyin da za mu bi ita ce zuwa kotu domin tabbatar da an yi abin da ya dace."

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Obi ta rikice kan zaɓen fitar da gwani a jihar Delta

Ya kuma yi nuni da yiwuwar samun sabon sauyin siyasa idan matsalar ba ta samu mafita cikin gaskiya da adalci ba.

“Akwai yiwuwar mu sake duba matsayarmu da kuma hanyar da za mu bi idan ba a samu daidaito ba,” in ji Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com