Yakin Iran: Trump Ya Ki Goyon bayan Isra'ila, Ya Gargadi Netanyahu da Khamenei
- Shugaba Donald Trump ya buƙaci Isra’ila da Iran su daina musayar hare-hare nan take, yana mai cewa za a cigaba da tattaunawa
- Kasashen biyu sun sake fara kai wa juna hare-hare karo na farko tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Afrilun 2026
- Hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya ta yi kira da a dawo teburin tattaunawa yayin da ake barin wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Iran da Isra’ila suna musayar hare-hare a karon farko tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Afrilun 2026, lamarin da ke barazanar sake tayar da yaƙi mai faɗi a Gabas ta Tsakiya.
Shugabannin duniya da kungiyoyi sun fara mayar da martani saboda tsoron kar lamarin ya jawo barkewar yaki da zai tsayar da lamura a yankin.

Kara karanta wannan
Bayan an ja kunnen Netanyahu, Iran ta kai harin makamai masu linzami zuwa Isra'ila

Source: Facebook
Gargadin da Donald Trump ya yi
Rahoton Sky News ya nuna cewa bayan shafe sa'o'i bai yi magana ba, Donald Trump ya ya fitar da sanarwa game da yakin Iran da Isra'ila.
Shugaban Amurka ya bukaci Isra’ila da Iran da:
“Ku tsagaita wuta cikin gaggawa”.
Al Jazeera ta wallafa cewa Trump ya kara da cewa:
“Tattaunawar ƙarshe kan ‘zaman lafiya’ na ci gaba, sai dai idan jahilci ko wauta suka shiga hanya suka hana hakan.”
Trump ya ce killace tashoshin jiragen ruwan sojojin Iran da Amurka ta yi zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniya ta ƙarshe.
Martanin Majalisar dinkin duniya
Rahotanni sun nuna cewa hukuma mai sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a koma tattaunawa.
Shugaban hukumar ya yi magana kan sababbin tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya da kuma yadda suke shafar tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
“Mun ga irin wannan a baya, kuma mun kuma ga lokutan da abubuwa suke fara yin sanyi kaɗan,”
In ji Rafael Grossi.
Rahotanni sun nuna cewa ya kara da cewa:
“Lokacin da ake ci gaba da luguden wuta, ba za a iya gudanar da bincike ba, amma akwai abubuwa da dama da za a iya yi. Abu mafi muhimmanci shi ne tattaunawa.”

Source: Getty Images
Grossi ya ce a halin yanzu yana hulɗa lokaci-lokaci da ministan harkokin wajen Iran, sai dai ya ce:
“Amma a zahiri hanyar sadarwar ta yanke.”
Houthi ta gargadi Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Houthi ta Yemen ta bayyana a ranar 8 ga Yunin 2026 cewa ta kai harin makami mai linzami Isra’ila tare da hana ta wucewa ta Tekun Maliya.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa duk wani jirgin ruwa da ke da alaƙa da Isra’ila za a dauke shi a matsayin abin da sojojin su za su kai wa farmaki.
Sanarwar ta tayar da damuwa kan yiwuwar sake samun cikas a hanyar safarar kayayyaki ta Tekun Maliya, wadda a baya ta sha fama da matsaloli sakamakon rikice-rikicen yankin.
Asali: Legit.ng