Su Wanene Ke Juya Akalar Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu? Minista Ya Koro Bayani

Su Wanene Ke Juya Akalar Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu? Minista Ya Koro Bayani

  • Ministan labarai, Mohammed Idris ya jaddada cewa babu wata ƙungiya ko mutum da ke juya shugaba Bola Tinubu ta karkashin kasa
  • Ya ce Tinubu ya tarar da tattalin arziki cikin mawuyacin hali, amma ya ɗauki matakai kamar cire tallafin mai domin farfaɗo da shi
  • Ministan ya lissafa manyan ayyukan gwamnatin Tinubu da suka hada da tituna, kafa asusun NELFUND da ba ma'aikata rancen kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa babu wani mutum ko kungiya da ke juya akalar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa, Shugaba Tinubu na saurarorin ra’ayoyi daban-daban, sai ya yanke shawara bisa hangen nesa kan abin da shi ne fi amfanuwa ga Najeriya.

Ministan labarai ya jaddada cewa babu wasu ko wani da ke juya akalar gwamnatin Tinubu ta karkashin kasa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @FMINONigeria
Asali: UGC

'Babu masu juya akalar Tinubu' - Minista

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin da yake gabatar da jawabi a taron kolin jam’iyyar APC, kamar yadda aka wallafa a shafin FMINONigeria na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya bayyana cewa:

"Yana da kyau a fahimci wannan shugaban. Kowa na da damar faɗar ra’ayinsa, kuma zai saurare ka, amma shi ne me yanke hukuncin karshe. Wannan abu ne da ya kamata kowa ya gane."

Game da taken taron, Idris ya ce Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar niyyar sauya Najeriya ta hanyar Renewed Hope, manufar da ya ce tana da karfin warware dukkanin matsaloli.

A cewar ministan:

“Manufar Renewed Hope ita ce inganta rayuwar 'yan Najeriya ta hanyar yanke muhimman matakan da za su fito da cikakken ƙarfin ƙasar nan, fiye da yadda aka taɓa gani.”

Tasirin matakan da Shugaba Tinubu ke dauka

Ya tunatar da cewa Shugaba Tinubu ya gaji Najeriya a lokacin da take cike da rudani, amma ya fara mulki cike da ƙwarin gwiwa da tsayayyen tunani.

Ministan ya ce ɗaya daga cikin matakan farko da shugaban ya ɗauka sun haɗa da cire tallafin man fetur da na musayar kuɗi, waɗanda suka kasance manyan matsaloli ga cigaban ƙasar.

Mohammed Idris ya jaddada cewa:

“Gaskiyar shugabanci na nufin iya ɗaukar matakai masu tsauri a matakin farko, amma wadanda za su haifar da ribar dogon lokaci.”

Ya ce sakamakon sauye-sauyen Tinubu, yanzu an samu manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafin rayuwa, da farfaɗo da sashen hakar ma’adinai da mai.

A Mohammed Idris:

"A matakin gwamnatin tarayya, ƙarin kudin shiga sun bai wa gwamnati damar fara manyan ayyuka da suka shafi rayuwar al'umma kai tsaye."
Ministan labarai ya lissafa manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa, Mohammed Idris. Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Minista ya jero manyan ayyukan Tinubu

Ministan ya bayyana manyan tituna guda huɗu da ake ginawa sune: titin Legas-Kalaba; Sokoto-Badagry; Kalaba-Abuja da Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe.

Ministan ya ce ɗalibai kusan 300,000 ne ke cin gajiyar asusun lamunin karatu na ƙasa (NELFUND), yayin da ma’aikata ke amfani da sabon tsarin karbar rance.

A fannin tsaro kuwa, Mohammed Idris ya ce:

"Sojojin Najeriya sun hallaka da kama dubban 'yan ta’adda, sun ceto kusan mutane 10,000, kuma sun samu sababbin jiragen sama 25, yayin da rundunar ruwa ta karɓi jiragen ruwa guda huɗu."

Akpabio ya kawo batun tsige Shugaba Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Godswill Akpabio ya tabo batun sanarwar tsige Shugaba Bola Tinubu yayin da yake jawabi a taron kolin jam’iyyar APC.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa babu wani yunkuri daga majalisa na tsige Tinubu, duba da yadda yake tafiyar da mulki cikin natsuwa da hangen nesa.

Ya ce duk da kalubalen tattalin arziki, Tinubu ya kafa Najeriya a kan hanya mai kyau, don haka suka ga ya cancanci ci gaba da mulki a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.