Bayan an Ja Kunnen Netanyahu, Iran Ta Kai Harin Makamai Masu Linzami zuwa Isra'ila
- Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila bayan Isra'ila ta yi kunnen kashi gane da gargaɗin da aka yi mata a baya
- Rundunar IRGC ta Iran ta ce harin gargadi ne ga Isra’ila kan ci gaba da kai farmaki a Beirut da sauran yankunan kasar Lebanon ba ji ba gani
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai tuntubi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu domin hana ƙarin ramuwar gayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran– Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila bayan gargadin da ta yi cewa dole ne Isra’ila ta dakatar da ci gaba da kai farmaki a Kudancin Lebanon ko kuma ta fuskanci ƙarin martani.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun fara ne da 10.00 na dare agogon ƙasar Isra’ila, lamarin da ya sa aka kunna ƙararrawar gaggawa a wurare da dama na ƙasar.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ruwaito cewa sojojin Isra’ila sun ce sun samu nasarar kakkabo dukkannin makaman da aka harba daga kasar Iran zuwa lokacin da suka fitar da sanarwar.
Iran ta kai harin gargaɗi Isra'ila
A ruwayar BBC, rundunar Iran ta IRGC ta tabbatar da kai harin, tana mai cewa ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai hari kan sansanin sojin sama na Ramat David.
Rundunar ta bayyana cewa harin martani ne ga abin da ta kira kisan gilla da kuma raba dubban mutane da muhallansu a yankunan Tyre da Nabatieh da ke kudancin Lebanon.
A cikin sanarwar da IRGC ta fitar, ta ce harin da aka kai wa Isra’ila gargadi ne kawai, tana mai cewa idan aka ci gaba da kai hare-hare kan Lebanon, za ta faɗaɗa martaninta.
Yadda Isra'ila ta fusata Iran
Mai bai wa Jagoran Addinin Iran shawara kan harkokin soji, Mohsen Rezaee, ya ce Iran ta sha bayyana cewa ba za ta lamunci karya yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma hare-haren da ake kai wa Lebanon ba.

Kara karanta wannan
Kotu ta dakatar da shari'ar da aka nemi soke rijistar ADC da wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya
Ya ce hare-haren da aka kai a wannan dare martani ne ga abin da ya kira cin zarafi da Isra’ila ke yi, yana mai gargadin cewa duk wani sabon hari zai fuskanci martani mafi tsauri.

Source: Facebook
Sai dai a ɓangarensa, Donald Trump ya bayyana cewa zai kira Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu domin roƙonsa kada ya mayar da martani ga Iran.
Trump ya ce hare-haren Iran ba su yi sanadiyyar jikkata kowa ba, yana mai fatan Isra’ila ba za ta mayar da martani ba saboda hakan na iya ƙara ruruta rikicin.
Ya ƙara da cewa Amurka da Iran na gab da cimma yarjejeniya mai muhimmanci, kuma ba ya son sababbin rikice-rikice su lalata ƙoƙarin da ake yi.
Martanin Iran ga Donald Trump
A baya, mun wallafa cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da batun cewa jagoran ƙasar zai gana da Donald Trump, bayan da Shugaban Amurka ya bayyana yiwuwar hakan.
Trump ya shaida cewa zai so ya gana da shi lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar ganawar, yana mai ƙarawa da cewa wataƙila za su gana a wani lokaci a nan gaba.
Sai dai babban jami'in diflomasiyyar Iran ya nuna rashin yiwuwar hakan a wata hira da kafafen yaɗa labarai da aka watsa, yana mai cewa ba abu ne mai yiwuwa ba Read more:
Asali: Legit.ng
