'Za Ku Rasa Kujerunku': Gwamna Ya Fusata da Muƙarrabansa ke Watse Masa a Taro
- Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya fusata da yadda wasu kwamishinoni ke barin wurin taro kafin shi, ya ce wannan rashin da'a ne
- Ya bayyana cewa dole kowane kwamishina ya zama ya na kusa da shi duk inda ya je, su tabbatar sun dawo da shi gida ko ofis
- A baya, gwamna Umo Eno ya riga ya yi wa wasu fiye da 200 gargadi saboda sun gaza halartar wani taro da ake gudanar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya fusata game da halayen wasu daga cikin mukarrabansa.
Gwamna Eno ya dage cewa dole ne hadimansa da kwamishinoni su halarci dukkan tarurrukansa tare da binsa a kowanne aiki na yau da kullum.

Asali: Twitter
Gwamna ya nuna damuwa kan halayen mukarrabansa
A wata sanarwa da Premium Times ta samu, Sakataren Gwamnatin Jihar, Enobong Uwah, ya ce gwamnan ya nuna bacin rai kan yadda mambobin majalisar zartarwa ke barin wurin taro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
“Wannan ya sabawa dokokin aiki, kuma ba za a lamunci hakan ko kadan ba."
Mista Eno, wanda ya taba rike mukamin kwamishinan filaye a karkashin Gwamna Udom Emmanuel, ya ce ba zai yarda da wannan halin raini ba.
A wani bidiyo da AIT ta wallafa, gwamnan ya yi barazanar korar duk kwamishinan da ya kasa kasancewa tare da shi ko tafiya ana tsaka da taro.
Gwamna Eno ya ce hakan tsantsar rashin biyayya ne wanda ke neman ruguza ayyukan da suka sanya a gaba.
Ya ce:
“Daga yau, kowa ya ji idan na kori kwamishina daga yankin ku, to rashin biyayya ce. Ba daidai ba ne a bar gwamna shi kaɗai.
“Ba zan sanar da inda zan je ba, dole ne kwamishina ya tabbatar da an dawo da ni ofis ko gidan gwamnati.
“Ina iya tsayawa a wani wuri, idan wata matsala ta taso, kwamishinan da abin ya shafa ne zai kula da ni a wajen.
“Idan muka je wani wuri, na bar wurin, kwamishina ba zai tafi inda ban sani ba, wannan aiki ne na cikakken lokaci."

Asali: Facebook
Gwamna ya gargaɗi kwamishinoninsa
Eno ya ce duk wanda da bai da lokacin yin wannan aiki, bai cancanci zama kwamishina ba tukuna saboda aikin gwamnati ba na 'yan hutu ba ne.
Ya tuna da cewa shi ma ya taba zama kwamishina, kuma bai taɓa barin gwamnansa a baya ba, komai wahala ko yawan aiki.
Ya kara da cewa:
“Yau ne karon karshe da zan faɗi haka, kuma ina yi ne a bainar jama’a. Idan na tsaya wani wuri, idan na nemi kwamishina, bai bayyana ba, to zai rasa aikinsa nan take."
Gwamna ya magantu kan yiwuwar barin PDP
A wani labarin, Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya sake nuna alamun ficewa daga jam'iyyar PDP.
Gwamna Eno ya ce a halin yanzun bai san wace jam'iyya zai koma ba a nan gaba, amma ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai yi wa kowa adalci.
Gwamnan ya nanata cewa shi gwamna ne na kowane dan Akwa Ibom ba tare da la'akari da jam'iyyun siyasa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng