'Har da APC': Atiku Ya Fadi Waɗanda Suke Shirin Haɗaka domin Kifar da Tinubu

'Har da APC': Atiku Ya Fadi Waɗanda Suke Shirin Haɗaka domin Kifar da Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi magana kan zaben 2027 domin shirin kifar da Bola Ahmed Tinubu
  • Atiku ya bayyana cewa jam'iyyun APC, PDP, LP da wasu jam’iyyu sun kafa kawance don kifar da gwamnatin a 2027
  • Ya ce rashin tsaro ya karu sosai, kuma kawancen zai hada kai wajen fuskantar gwamnatin da ya kira mara nagarta kuma ta gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fadi shirin da suke yi game da zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Atiku ya bayyana cewa jam'iyyun APC, PDP, LP da wasu sun kafa kawance don kifar da Bola Tinubu da ake zargi da kassara tattalin arziki.

Atiku ya yi magana kan haɗaka a 2027
Atiku ya faɗi jam'iyyun da suka shirin haɗaka a 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 14 ga watan Mayun 2026 a Abuja yayin ziyarar wasu shugabanni daga yankin Kogi ta Gabas, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyun adawa na fuskantar matsaloli a 2027

A baya, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga APC kuma yana tare da shirin kawance a karkashin SDP domin kwace mulki a hannun Tinubu.

Haka kuma, tsohon Ministan Matasa da Wasanni a mulkin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya bar APC saboda alkawura da ba a cika ba da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.

Duk da yunkurin kifar da gwamnatin APC a 2027, PDP na fama da sauya shekar da suka hada da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da Ifeanyi Okowa da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

A baya-bayan nan, wasu ‘yan majalisar wakilai da na dattijai sun bar PDP zuwa APC domin shiryawa zaben 2027 mai zuwa wanda ya sake nakasa jam'iyyun adawa.

A Kano ma, wasu yan majalisu da jiga-jigan jam'iyyarsu ta NNPP sun sauya sheka zuwa APC wanda suka alakanta haka da rigima a jam'iyyar da suka baro.

Atiku ya magantu kan shirin haɗaka a Najeriya
Atiku ya fadi shirin kifar da gwamnatin Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Getty Images

2027: Atiku ya magantu kan shirin haɗaka

'Dan takarar shugaban kasa a PDP a 2023 ya fadi haka ne yayin da jiga-jigai daga PDP suka kai masa ziyara karkashin jagorancin Simon Achuba.

Ya ce an kafa kawancen jam’iyyun ne domin su fuskanci gwamnatin Shugaba Tinubu da karfi daya a matsayin tsintsiya madaurinki guda.

Yayin da yake magana kan tabarbarewar tsaro, Atiku ya ce:

“Ina so ku fahimta cewa ya rage mana, ku shugabanni ne a yankunanku.
“Mun kafa kawance. Duka manyan jam’iyyun siyasa sun shiga. APC, PDP, LP muna tare, wannan ce hanya wajen fuskantar gwamnati maras nagarta.”

Boko Haram: Atiku ya yabawa gwamnatin Obasanjo

Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yabawa mulkin Cif Olusegun Obasanjo kan murkushe yan kungiyar Boko Haram.

Atiku ya ce Obasanjo ya murkushe su a cikin makonni kadan tun farkon bayyanar kungiyar a shekarar 2002 wanda daga bisani suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Atiku ya yabawa salon mulkin Obasanjo inda ya kara da cewa mai gidan nasa ya yi tsayin daka wajen korar kungiyar Boko Haram daga garuruwan da suke.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.