Yadda EFCC Ta Yi Nasarar Kama Ministan Buhari a inda ba a Yi Tsammani ba
- Tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman, wanda kotu ta yanke wa hukunci ya shiga hannu bayan hukumar EFCC
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an cafke Mamman da wasu mutum biyu da ke boye shi, bayan jami’ai sun bi sawunsa cikin sirri
- EFCC ta bayyana cewa Mamman ya rika sauya layukan waya da wayoyi domin guje wa kama shi, amma jami’ai suka gano maboyarsa a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wata babbar Kotu a Najeriya ta yanke wa tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari.
Mamman ya shiga hannun jami’an Hukumar EFCC ranar Talata bayan watanni yana boye daga hukuncin kotu da aka yanke masa.

Source: Facebook
Wane lokaci aka cafke Saleh Mamman?
An kama Mamman ne a yankin Rigasa da ke Kaduna da misalin karfe 3:30 na dare, kamar yadda shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Jami'an EFCC sun kutsa cikin gida a Kaduna, sun cafko ministan Buhari da ake nema
Kotu ta tarayya da ke Abuja ta yanke wa Mamman hukuncin shekaru 75 a gidan yari bayan samunsa da laifukan almundahana da karkatar kudade.
Mai shari’a Omotosho ya same shi da laifuka guda 12 da suka shafi badakalar biliyan N33.8 daga ayyukan wutar lantarkin Mambilla da Zungeru.
Olukoyede ya ce an kama Saleh Mamman tare da wasu mutum biyu da ake zargin suna taimaka masa wajen boyewa daga jami’an tsaro da bincike.
Ya kara da cewa gidan da aka kama tsohon ministan yana karkashin bincike domin gano yadda aka rika ba shi kariya tsawon lokaci.

Source: Facebook
Gargaɗin da EFCC ta yi wa al'umma
Shugaban EFCC ya bayyana kama Mamman a matsayin babban nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin Najeriya baki daya.
Ya ce duk wanda ya wawuri dukiyar gwamnati ko ta kasa ba zai tsira daga hukunci ba domin jami’an EFCC za su gano shi, cewar Punch.
Wata majiya ta bayyana cewa Mamman ya rika canza lambobin waya da amfani da layuka daban-daban domin kaucewa bin sawunsa da jami’ai ke yi.
Sai dai jami’an EFCC sun samu nasarar gano maboyarsa bayan dogon bincike, lamarin da ya kai ga cafke shi a Kaduna cikin dare.
Olukoyede ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa EFCC za ta ci gaba da binciken duk masu hannu wajen karkatar da kudaden jama’a da rashawa.
Ya jaddada cewa hukumarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani mutum da aka samu da laifin cin dukiyar kasa.
EFCC na neman tsohuwar minista ruwa a kallo
Mun ba ku labarin cewa hukumar EFCC ta ayyana neman tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dukiyar kasa.
A wata sanarwa da ta fitar, EFCC ta ce wuri na karshe da aka ga Sadiya shi ne a Abuja, inda ta roki 'yan Najeriya su kai rahoto idan sun ganta.
A ranar 16 ga Afrilu, 2026, babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja ta bayar da sammacin kama Sadiya bayan ta ki halartar zaman kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
