"Kafin Ka Nemi Shugaban Kasa," Akpabio Ya Fadawa Obi abin da Ya Kamata Ya Yi
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya soki Peter Obi kan maganar da ya yi cewa "aikin 'yan mazan jiya ya zama na banza"
- Godswill Akpabio ya bukaci Peter Obi da ya fara magance rikice-rikicen da ke addabar jam'iyyar LP kafin ya ce zai shugabanci Najeriya
- Shugaban majalisar ya kuma zayyano nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamna, ya ce ya biya wa Musulmi 5,800 kudin aikin Hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi martani mai zafi ga Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a 2023, kan kalaman da ya yi na cewa “aikin 'yan mazan jiya ya zama na banza”.
Akpabio ya shawarci Obi da ya fara warware matsalolin cikin gidan “ƙaramar jam’iyyarsa” kafin ya yi burin zama shugaban kasar Najeriya.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Akpabio ya yi martanin ne a ranar Alhamis a lokacin bankwana da gawar mariyagyi tsohon ministan yaɗa labarai kuma jagoran Kudu maso Kudu, Cif Edwin Clark.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar ya bayyana cewa idan Obi ba zai iya magance matsalolin LP ba, to kuwa ba shi da cancantar mulkin ƙasa mai girma kamar Najeriya.
Asalin abin da Peter Obi ya faɗa
A jawabin da ya gabatar ranar Laraba a taron lacca na girmama marigayi Cif Clark a Abuja, Obi ya yaba da “rayuwar Cif Clark ta jarumtaka, sadaukarwa, da girmamawa”.
Ya kuma nuna damuwa game da halin da Najeriya ke ciki a yanzu, yana mai cewa sadaukarwar shugabannin da suka gabata kamar Janar Yakubu Gowon da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan sun tashi a banza.
Obi ya nuna takaici kan rashin zanga-zangar da aka yi lokacin da aka samu hauhawar farashin fetur na baya-bayan nan.
Dan takarar shugaban kasar ya ce an yi zanga zanga lokacin mulkin Jonathan kan hauhawar farashin man fetur.
Ya soki gwamnatin Najeriya, yana mai cewa demokraɗiyya ta mutu a kasar, sannan ya nuna alhini kan zargin da ake yi cewa sukar da yake yi wa gwamnati ya zama "shafawa ƙasa baƙin fenti".
Akpabio ya yi martani ga kalaman Obi
A martaninsa, Akpabio ya ce:
“Idan ba za ku iya warware rikicin jam’iyyar ku ta LP ba, ta yaya za ku iya magance rikicin Boko Haram ko wasu manyan batutuwan ƙasa?
“Ina kira ga masu burin jagorancin Najeriya da su fara magance matsalolin da ke cikin jam’iyyunsu."

Asali: Facebook
Ya kuma yi amfani da damar wajen nuna nasarorin da ya samu a matsayinsa na tsohon gwamna.
Ya ce:
“Zan iya bugun kirji game da manyan titunan da muka gina a birnina, mun gina asibitocin ƙasa da ƙasa da ofisoshin gwamna na zamani.
“Na kuma ƙaddamar da ilimi kyauta kuma na yi aiki don haɗin kan addini ta hanyar ɗaukar nauyin Musulmi sama da 5,800 da Kiristoci kusan 15,000 zuwa aikin Hajji, Rome da Urushalima.
Akpabio ya yabawa Obi a bikin ɗan Barau
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa ya yi ruwan kalaman yabo kan Peter Obi da ya halarci ɗaurin auren ɗan Sanata Barau Jibrin.
Godswill Akpabio ya bayyana zuwan Peter Obi wajen ɗaurin auren a matsayin alamun da ke nuna akwai haɗin kai a ƙasar nan duk da bambancin ra'ayin siyasa.
Ɗaurin auren na Abdullahi Barau da amaryarsa Bilkisu Aliyu Sani Madaki, ya samu halartar manyan ƙusoshi a ƙasar nan, ciki har da shugaban jam'iyyar APC na kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng