Jam'iyyar SDP Ta Zo da Sabon Shiri, Ta Saɓawa Atiku da El Rufai kan Kifar da Tinubu a 2027
- Jam'iyyar SDP mai adawa ta bayyana cewa ga dukkan alamu ita za ta lashe zaɓen shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2027
- Mataimakin shugaban SDP na Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara ya ce idan Allah ya yarda za su kwace mulki daga hannun Bola Tinubu
- Dogara ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa SDP baya kuma su yi rijistar zama cikakkun ƴan jam'iyya a mazaɓunsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara kankama a Najeriya, jam'iyyar SDP ta bayyana kwarin gwiwar cewa ita za ta karɓi mulkin ƙasar nan.
SDP ta ce tana da ƙwarin gwiwar cewa za ta karbi mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a 2027.

Asali: Twitter
Mataimakin shugaban SDP na kasa a yankin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara, ne ya bayyana hakan a taron jam'iyya da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Nasarawa, Tribune Nigeria ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'SDP za ta kwace mulki da ikon Allah'
Dogara ya ce jam’iyyar na kokarin fadada yawan mambobinta a fadin kasar nan, yana mai jaddada cewa SDP ta zama abar kauna ga ‘yan Najeriya a halin yanzu.
Abubakar Dogara ya ce:
“Mu na gudanar da taruka tun daga matakin shiyya, matakin kasa, mazabu, matakin jiha har zuwa kananan hukumomi.
“Wannan na daga cikin shiri da muke yi domin karbar mulki a 2027, idan Allah ya yarda. Adadin mambobinmu kullum yana karewa saboda yawan masu shiga jam’iyyar.
Yadda ƴan Najeriya ke son shiga SDP
Dogara ya kara da cewa mutane da dama, ciki har da manema labarai, na nuna sha’awar shiga jam’iyyar SDP.
Mataimakin shugaban SDP ya yaba da goyon bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Hon. Jonathan Gaza, Prince Adewale Adebayo, da Hon. Femi Olaniyi Ferrari.
Prince Adewale Adebayo, shi ne ya yi takarar shugaban ƙasa a inuwar SDP a zaben da Bola Tinubu ya samu nasara a 2023.

Asali: Twitter
Ra'ayin SDP ta saɓawa shirin Atiku, El-Rufai
Abubakar Dogara ya ce daga cikin matsayar da aka cimma a taron shi ne SDP ba za ta sake mika tsarin jam’iyyar ga wasu mutane ba kamar yadda aka saba, domin kare martabarta da mambobinta.
“SDP ita ce zabin yan Najeriya yanzu. Sakonmu ga ‘yan kasa shi ne su fito kwansu da kwarkwata su shiga jam’iyyarmu mai albarka.
“Da farko, su mara wa shugabancin SDP baya ta hanyar bin kundin dokokin jam'iyya, wanda ke bukatar kowane dan jam’iyya ya yi rijista daga matakin mazabu zuwa jiha da matakin kasa,” in ji Dogara.
Wani ɗan PDP da ya koma SDP lokacin da El-Rufai ya sauya sheƙa, Auwal Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa sun shirya tsaf don tunkarar zaɓen 2027.
Auwal, wanda ke neman takarar ɗan majalisar wakilai ya ce za su haɗa kan mutane, matasa da mata domin nasarar SDP a zaɓe mai zuwa.
"In sha Allah, Najeriya za ta buɗe sabon shafi, za mu zama silar share hawayen ƴan Najeriya, muna fatan mutane za su ba mu haɗin kai wajen kawar da APC," in ji shi.
Jam'iyyar SDP ta ba mutum 3 muƙami a NWC
A wani labarin, kun ji cewa SDP ta zaɓi sababbin mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa daga Arewa da Kudu, ta sanar da sabon sakataren kuɗi.
Sakataren SDP na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba ne ya bayyan sunayen waɗanda aka naɗa a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.
SDP ta yi wannan gyara a kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa yayin da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 ya ƙara kankama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng