Nadin da Tinubu Ya Yi, Ya Jawo Cikas, Rikici Ya Kunno Kai a Jam'iyyar APC

Nadin da Tinubu Ya Yi, Ya Jawo Cikas, Rikici Ya Kunno Kai a Jam'iyyar APC

  • Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta caccaki masu shirin zanga-zanga kan rashin goyon bayan nadin Cyril Tsenyil a NCDC
  • Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga ya ce wadanda ke adawa da nadin ba 'yan yankin ba ne, kuma suna aiki ne da jam’iyyar adawa
  • Kungiyar matasa daga Filato ta bukaci a janye nadin shugaban saboda zargin cewa ba ya wakiltar muradun jama’ar jihar Filato ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta yi watsi da zanga-zangar da wasu ke yi kan nadin Cyril Tsenyil a matsayin Darakta Janar na Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC).

Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yana mai cewa zanga-zangar ta fito daga wasu mutanen bogi marasa tushe a yankin.

Tinubu
Nadin da Tinubu ya yi a Filato ya bar baya da kura Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa Zazzaga ya zargi masu zanga-zangar da kasancewa cikin tsarin jam’iyyar adawa domin hana hukumar cika ayyukan da aka kafa ta domin su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, zanga-zangar na da nufin janyo cikas ga aikin hukumar da aka kafa domin inganta cigaban yankin Arewa ta Tsakiya.

'Yan APC sun yi zanga-zanga saboda nadin Tsenyil

Daily Post ta ruwaito cewa kungiyar da ta kira kanta Concerned Plateau Youth Forum, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya soke nadin Tsenyil, su na mai cewa ba ya wakiltar muradun Filato.

Wakilin kungiyar, Danladi Pam, ya sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a Abuja don nuna rashin amincewa da nadin.

A martaninsu, Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta bayyana wadannan masu zanga-zangar a matsayin 'yan siyasa da ke kokarin bata sunan gwamnatin Tinubu da hana ci gaban yankin.

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Cyril Tsenyil a matsayin Manajan daraktan NCDC Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ta ce:

"Mun tabbata cewa ba ‘yan asalin Filato ko Arewa ta Tsakiya ba ne. Babu wani mai hankali daga wannan yanki da zai hana ci gaba da ake muradi daga hukumar NCDC, musamman karkashin kwararren mutum irin Cyril Tsenyil."

Kungiyar APC ta goyi bayan Tsenyil

Zazzaga ya kara da bayyana cewa Tsenyil ya cancanci nadin da aka yi masa duba da tarihin aikin sa da sadaukarwa ga jam’iyyar APC.

Ya bayyana Tsenyil a matsayin kwararren akanta wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga nasarar jam’iyyar da kuma gwamnatin Tinubu.

Kungiyar ta yaba da hangen nesa da shugaban kasa Tinubu ya nuna wajen nadin Tsenyil, ta ce hakan zai taimaka wajen cimma burin yankin na bayar da kuri’u miliyan shida a zaben 2027.

Wanene Cyril Tsenyil?

Cyril Tsenyil sabon Darakta Janar na Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC) mutum ne mai kwarewa da gogewa a fannin gudanarwa da siyasa.

Ya fito ne daga jihar Filato, ya yi fice a bangaren siyasa da al’amuran ci gaban al’umma. Tsenyil ya yi karatu a manyan makarantu masu daraja, kuma yana da kwarewa ta musamman wajen jagoranci da tsare-tsare na gwamnati.

A shekaru da dama da ya yi yana aiki, ya samu damar nuna bajintarsa wajen kawo sauyi da inganta ayyukan gwamnati a matakai daban-daban, rahoton The Guardian.

Har ila yau, yana da kyakkyawar dangantaka da jam’iyyar APC, ya bayar da gudunmawa mai yawa wajen samun nasarorin jam’iyyar a jihar Filato da yankin Arewa ta Tsakiya baki daya.

Nadin Tsenyil a matsayin Darakta Janar na NCDC na nufin kawo ci gaba da bunkasa yankin Arewa ta Tsakiya, musamman ta fuskar tsare-tsare da ayyukan raya kasa.

Duk da yake akwai wasu suka nuna rashin amincewa da nadin, kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta tabbatar da cewa Tsenyil ya cancanci wannan mukami saboda gogewarsa da sadaukarwarsa wajen tafiyar da al’amuran siyasa da ci gaba a yankin.

Saboda haka, Cyril Tsenyil na daga cikin manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Arewa ta Tsakiya, kuma nadinsa na daga cikin matakai na tabbatar da ci gaban yankin karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jam'iyyar APC ta yiwa Atiku martani

A baya, mun wallafa cewa APC ta yi watsi da ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya ce wasu daga cikin 'yan jam’iyyar mai mulki suna cikin hadakar adawa.

Atiku ya yi bayyana cewa wasu mutane daga jam’iyyun APC, PDP, LP da sauran jam’iyyu suna cikin tafiyar hadakar adawa da ke da nufin fitar da Bola Tinubu daga ofis a 2027.

A martanin jam’iyyar APC, Daraktan Yaɗa Labaranta, Bala Ibrahim, ya bayyana ikirarin Atiku a matsayin rudu da kokarin janyo hargitsi, sannan ya ce babu kamshin gaskiya a labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.