SDP: 'Yan NNPP Sun Koma Tafiyar El Rufa'i a Mazabar Kwankwaso a Kano

SDP: 'Yan NNPP Sun Koma Tafiyar El Rufa'i a Mazabar Kwankwaso a Kano

  • Jam’iyyar SDP ta karbi tarin matasa daga NNPP a Kwankwaso, karamar hukumar Madobi, inda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar farin doki
  • Haka zalika a Owerri, tsohon shugaban jam’iyyar AA da mataimakinsa da wasu mutane sama da 20 sun fice daga jam’iyyarsu zuwa SDP
  • Shugabannin SDP sun yaba da sauya shekar, suna cewa hakan alama ce ta yadda al’umma ke bukatar sabuwar tafiya ta shugabanci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Matasa da dama a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP

Lamarin ya faru ne a mazabar Kwankwaso da ke kauyen Danyanta, matasa da dama, mafi yawansu daga jam’iyyar NNPP, suka mika wuya ga jam’iyyar SDP mai alamar farin doki.

SDP Kano
'Yan NNPP sun koma SDP a mazabar Kwankwaso. Hoto: SDP National Update
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da jam'iyyar SDP ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shugaban SDP na Madobi, Kwamared Isah Saidu Kwankwaso, matakin matasan ya nuna yadda jama’a ke fara fahimtar nagartar tsare-tsaren jam’iyyar.

'Manufofin SDP sun fara karbuwa' – Isah Kwankwaso

Isah Kwankwaso ya bayyana cewa burin jam’iyyar shi ne ganin kowace mazaba a Madobi ta hade karkashin tutar SDP kafin babban zaben 2027.

Ya ce:

“Mun sa rai kuma muna da yakini cewa nan gaba kadan, kowace jam’iyya a Madobi za ta rungumi SDP domin wannan ita ce jam’iyyar da ke da tsari da hangen nesa na kawo cigaba mai dorewa.”

Ya jaddada cewa SDP ba wai jam’iyyar siyasa ba ce kawai, sai dai wata tafiya ce ta ceto al’umma daga halin da suka tsinci kansu a ciki na rashin ingantaccen shugabanci.

Jiga-jigan AA sun koma SDP a Owerri

A wani bangare na daban, jam’iyyar SDP ta samu karuwa a garin Owerri, jihar Imo da ke Kudancin Najeriya.

Tsohon shugaban jam'iyyar AA, Emeka Onwuemenyi da mataimakinsa Orji Nneji, sun fice daga jam’iyyarsu tare da wasu mambobi sama da 20 sun koma SDP.

A lokacin sauya shekar, Emeka Onwuemenyi ya ce jam’iyyar AA ta kauce turbar da ta sa shi shiga cikinta.

SDP Imo
'Yan AA sun koma SDP a Imo. Hoto: SDP National Update
Asali: Facebook

Shugaban SDP na Owerri, Hon. Ofoma Desmond, ya karbi sababbin mambobin hannu bibbiyu, inda ya ce sun zabi jam’iyyar da ke da alkibla da mafita ga matsalolin al’umma.

Ya bukaci dukkan mambobin su koma mazabunsu su ci gaba da wayar da kai da karfafa jam’iyyar domin fuskantar zaben 2027.

2027: An nemi Atiku ya hakura da takara

A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce Nasir El-Rufa'i ba zai iya jagorantar tafiyar 'yan adawa a Najeriya ba a halin yanzu.

Injiniya Buba Galadima ya kuma yi kira ga Atiku Abubakar da ya hakura da maganar takara a zaben shekarar 2027 domin ba sababbin jini dama.

Baya ga haka, Buba Galadima ya karyata rade radin cewa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana yi wa Bola Tinubu aiki ta karkashin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng