Kano: Duk da Gargadin Kwankwaso, 'Yan Majalisar NNPP 2 Sun Koma APC
- ‘Yan majalisar wakilai biyu daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC saboda rikicin cikin gida da ke addabar NNPP
- Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Usman Alhasan Rurum, wadanda ke wakiltar mazabun Rano/Bunkure/Kibiya da Karaye/Rogo sun sauya sheka
- Sauya shekar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan NNPP ciki har da Sanata Kawu Sumaila suka koma APC a Kano saboda wasu dalilai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta tabbatar da sauya shekar Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Usman Alhasan Rurum daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a zaman majalisar na yau Alhamis.
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikun sauya shekar a gaban ‘yan majalisa.

Asali: Facebook
Jaridar the Cable ta wallafa cewa ‘yan majalisar biyun sun danganta sauya shekar da rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyarsu ta NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauya shekar ya kara nuna alamun tsamin dangantaka da rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar jam’iyyar NNPP musamman a Kano, inda ta samu karbuwa.
Jam'iyyar APC ta tarbi ‘yan majalisar NNPP
A yayin sauya shekar, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci zaman majalisar tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar domin nuna maraba da sababbin ‘yan majalisar.
The Nation ta rahoto cewa wani dan majalisa daga Osun, Oluwole Oke, ya kammala komawa APC a hukumance, lamarin da ke kara nuna yadda jam’iyyar ke karuwa a daukacin fadin kasar nan.
Ganduje da sauran shugabannin APC sun bayyana jin dadinsu da sauya shekar da 'yan majalisar suka yi.
Jam'iyyar APC na cigaba da karbar masu sauya sheka da suka hada da gwamnoni, Sanatoci da 'yan majalisar wakilai.
Gargadin Kwankwaso kan fita daga NNPP
Sauya shekar ya zo ne kasa da mako bayan da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ya yi kakkausar suka ga duk wadanda ke sauya sheka daga NNPP zuwa APC bayan samun nasara a zabe.
Kwankwaso ya bayyana cewa irin wadannan matakai cin amanar jam’iyya ne, yana mai kira da a daina amfani da jam’iyya don samun nasara sannan a juya mata baya.
Sai dai duk da gargadin, NNPP na ci gaba da fuskantar kalubale a Kano, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar ke komawa APC, suna danganta matsayinsu da rikici da rashin shugabanci nagari.

Asali: Facebook
Me zai biyo baya a NNPP a Kano?
Ana ganin sauya shekar a matsayin karin koma baya ga NNPP musamman a Kano, inda take da gwamnati da yawancin ‘yan majalisa.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan jagororin NNPP a Kano domin ganin matakin da za su dauka a kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi.
Tun kwanakin baya aka ji baraka ta shiga tsakanin Madugun Kwankwasiyya da wasu mutanensa a NNPP kamar Hon. Ali Madakin Gini.
Kalubalen da NNPP ke fuskanta
Jam’iyyar NNPP na fuskantar babban kalubale na rasa mambobi musamman manyan ‘yan majalisa da wasu fitattun shugabanni a Kano, wadda ta kasance wata muhimmiyar cibiyar jam’iyyar.
Sauya shekar da ‘yan majalisar wakilai biyu suka yi zuwa APC, tare da barin wasu sanannun mutane kamar Sanata Kawu Sumaila, na nuna akwai rikici da rashin jituwa a cikin jam’iyyar.
Wannan na iya jefa makomar NNPP cikin hatsari, musamman ma idan rikicin ya ci gaba ba tare da an sami gyara ba.
Rashin kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar zai iya sa jama’a su rasa amincewa da shugabancinsu, musamman a jihohin da jam’iyyar ke da karfi kamar Kano.
Hakan na iya haifar da raguwar goyon baya da kuma zubar da kuri’u a zabukan gaba, wanda zai ba APC damar kara karfi a wannan yanki mai muhimmanci.
Saboda haka, NNPP na bukatar daukar matakai na gaggawa wajen sasanta rikice-rikicen cikin gida, da kuma tabbatar da shugabanci mai inganci domin dawo da amincewar ‘yan jam’iyya da magoya bayanta.
Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya karbi wasu 'yan jam'iyyar NNPP da suka sauya sheka a jihar Kano zuwa APC.
Sanata Kawu Sumaila ya raka wasu tsofaffin kansiloli aSumaila da suka fita daga NNPP zuwa APC a ofishin Sanata Barau.
Wata kungiya mai suna 'Abba Kawai' ta ajiye siyasar Kwankwasiyya ta koma jam'iyyar APC ta hannun Sanata Barau Jibrin a Abuja.
Asali: Legit.ng