Ta Faru Ta Kare: PDP Ta Ajiye Atiku, Ta Fadi Wanda Za Ta Marawa baya a 2027
- Jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa ta bayyana cewa za ta marawa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 mai zuwa
- Shugaban PDP na Bayelsa ya bukaci Gwamna Douye Diri ya fito ya bayyana matsayinsa, ya ce mafi yawan gwamnonin Kudu na tare da Tinubu
- George Turnah ya ce Tinubu na shimfida ayyukan da ya kamata, don haka bai kamata a fara maganar sauya shugaba mai yi wa jama'a aiki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa - A yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke kara karatowa, jam'iyyar PDP ta fito ta bayyana cewa za ta marawa Shugaba Bola Tinubu baya a zaben.
Sakataren PDP na shiyyar Kudu maso Kudu kuma shugaban riko na jam'iyyar a jihar Bayela, George Turnah ya ce Tinubu za su zaba, ba wani dan takara ba.

Asali: Facebook
Bayelsa: PDP za ta goyi bayan Tinubu a 2027
A rahoton da jaridar Punch ta fitar, an ji cewa George Turnah ya shaida wa gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Doyte Diri cewa za su bi bayan Tinubu, ko da yarda ko bai yarda ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran PDP na shiyyar ya bayyana cewa mafi yawancin gwamnonin yankin Kudu maso Kudu suna marawa Tinubu baya, duk da cewa wasu daga cikinsu ba 'yan APC ba ne.
George Turnah, wanda shi ne jagoran kungiyar New Associates, wata ƙungiya mai goyon bayan Nyesom Wike da aka kaddamar a Bayelsa a karshen makon nan, ya bukaci Gwamna Diri da ya bayyana matsayinsa nan take.
Ya bayyana cewa ya shirya taron gangamin da aka yi a Yenagoa a ranar Asabar domin nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu bisa nada ’ya’yan yankin Niger Delta a muƙaman gwamnati.
Jam'iyyar PDP na tare da wanda Wike yake so
Da ya ke kira ga gwamnan ya fadi matsayarsa kan wanda zai marawa baya a 2027, shugaban jam'iyyar na PDP ya ce:
“Ina kira ga Gwamna Douye Diri da ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027, domin mutanen Bayelsa suna son sani tun da wuri.
“Idan yana goyon bayan Shugaba Tinubu, to ya fito ya faɗa. Amma idan yana tare da wani dan takara daban, muna son sani. Wannan zai bamu damar yanke shawarar ko za mu bi shi ko a’a.
“Jagoran da ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a fili shi ne Nyesom Wike. Idan gwamnan mu ya fito gobe ya ce yana goyon bayan Tinubu, za mu yi aiki tare da shi. Idan kuma ba haka ba, mu da kanmu za mu hada kai domin mara wa Tinubu baya.
“A shekarar 2019, gwamnonin Kudu sun gana a Asaba inda suka amince mulki ya koma Kudu. Duk da haka wasu daga cikinsu suka bijire. Amma a ƙarshe, Tinubu daga Kudu ne ya zama shugaban ƙasa.

Asali: Facebook
"Babu bukatar sauya shugaba Tinubu" - PDP
Shugaban jam'iyyar ta PDP a Kudu maso Kudu ya ci gaba da cewa:
“Ko da yake Tinubu ba dan jam’iyyata PDP ba ne, amma idan an zabi shugaba, to shugaban Najeriya ne gaba ɗaya, dole mu mara masa baya.
“Adawa ba ta nufin a hana shugaba cin nasara ba. Idan shugaba ya yi nasara, al’umma ke amfana. Adawa ce ya kamata ta sa shugabanni su cika alkawura ga jama’a.
“Idan shugaba yana aiki yadda ya dace, babu buƙatar a gaggauta neman wani sauyi. Idan lokaci ya yi, PDP za ta yanke shawara kan matakin da ya dace.”
Sau biyu kenan Atiku Abubakar na samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, kuma duk da haka bai taba samun nasarar lashe zabe ba.
Tinubu ya kara karfi a jihar Jigawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya kara karfi a Jigawa yayin da daruruwan magoya bayan PDP, NNPP suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar.
Gwamna Namadi ya tabbatar wa sababbin mambobin adalci da damar bada gudummawa, yana mai ƙarfafa su su yada manufofin APC.
Jagoran masu sauya sheƙar, Idris Maikura, ya ce sun ga ayyukan Namadi kuma sun yarda jam'iyyar APC ce mafita ta ci gaban jihar Jigawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng