Bayan Ta Karɓi Sanata daga PDP, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Yin Babban Kamu a Najeriya

Bayan Ta Karɓi Sanata daga PDP, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Yin Babban Kamu a Najeriya

  • Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar LP a jihar Bayelsa, Udengs Eradiri ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulkin ƙasa a hukumance
  • Da ya sauya-sheka, Mista Eradiri ya yankin katin APC a gunduma ta 10, mazaɓa ta 2 a ƙaramar hukumar Yenagoa da ke jihar Bayelsa
  • Ya yabawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu bisa ayyukan ci gaban da yake yi a mazaɓarsa da Neja Delta gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar LP a Jihar Bayelsa, Udengs Eradiri, ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Ya danganta matakin da ya dauka da himmar shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen zuba ayyukan ci gaba a yankinsa na Agudiama/Ekpetiama a ƙaramar hukumar Yenagoa.

Udengs Eradiri.
Tsohon dan takarar gwamnan Bayelsa a LP ya sauya sheka zuwa APC Hoto: Udengs Eradiri
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa Mista Eradiri, ya yi rajista da APC a gunduma ta 10, mazaɓa ta 2 da ke yankin ƙaramar hukumar Yenagoa a Bayelsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eradiri: "Gwamnatin APC na zuba ayyukan alheri"

Ya jaddada muhimman ayyuka da gwamnatin Tinubu ta aiwatar ta hannun Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da Dr. Samuel Ogbuku ke jagoranta.

Wadannan ayyuka sun hada da samar da ruwan sha, kare gabar teku daga rushewa, fitilun tituna na hasken rana, da kuma titi mai tsawon kilomita daya.

Ya bayyana cewa ayyukan ba yankin kaɗai suka amfana da su ba, har ma da sauran yankuna da dama a Neja Delta.

Udengs Eradiri ya jinjina wa kokarin hukumar NDDC da rundunar tsaro bisa rawar da suka taka wajen kawo zaman lafiya da ci gaba a yankin.

Bugu da kari, Eradiri ya yabawa ayyukan ci gaba da gwamnati Tinubu ta fara, ciki har da shirin gyaran makarantar sakandare ta yankinsu da kuma gina sansanin ƴan bautar ƙasa watau NYSC.

Eradiri ya yabawa shugaba Bola Tinubu

Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa rattaba hannu kan dokar kafa Jami’ar Maritime da amincewa da kafa Jami’ar Fasaha da Muhalli a Ogoni.

A matsayinsa na tsohon kwamishinan matasa, Eradiri ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa nada ‘yan asalin Bayelsa a manyan mukamai.

Eradiri ya gode wa ƴaƴan APC a Bayelsa bisa kyakkyawar tarbar da suka masa, tare da alkawarin yin aiki da dukkan shugabannin jam’iyyar domin kara karfafa APC a jihar da kasa baki daya.

“A yankina kaɗai gwamnatin APC ta mana aikin ruwa, aikin kare gabar teku, an sa fitilun da ke amfani da hasken rana da kuma gina hanyar mai tsawon kilomita daya.
"Haka kuma, gwamnatin APC ta yi alkawarin gudanar da wasu ayyuka kamar gyaran makarantar mu ta sakandare da gina sansanin masu hidimar kasa (NYSC).”

- Udengs Eradiri.

APC ta fara hangen nasara a jihar Anambra

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aniyarsa na ganin jam'iyyar ta karɓe mulki a jihar Anambra.

Ganduje ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar masu arziki a jihar su yi amfani da dukiyarsu wajen bunƙasa APC maimakon su yi ƙoƙarin tarwatsa ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262