Tsautsayi: Wani Bawan Allah Ya Rasu da Bam Ya Tarwatse a kan Titin Zamfara
- Wani bam da aka dasa a kan hanya ya tarwatse a titin Anka zuwa Bagega a jihar Zamfara, inda mutum guda ya rasa ransa
- Lamarin ya faru ne kwanaki uku kacal bayan sace dattawa 39 lokacin da suka je zaman sulhu da 'yan bindiga a karamar hukuma Maradun
- Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta tabbatar da tashin bam din, ta tura jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Wani mutumi ya rasa ransa yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon fashewar bam da ake zargin an dasa a gefen titin Anka zuwa Bagega a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata lokacin da bam din ya tarwatse da wata motar haya kirar Golf-3 Wagon da ke dauke da fasinjoji daga kauyen Bagega zuwa garin Anka.

Source: Facebook
Yadda bam ya tashi da matafiya
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen Bagega mai suna Malam Abdul ya bayyana cewa motar ta taka bam din ne yayin da ta zo wucewa ta titin.
A cewarsa, daya daga cikin fasinjojin ya mutu nan take sakamakon karfin fashewar, yayin da wasu mutum bakwai suka samu raunuka daban-daban, kuma suna karbar magani a wani asibiti da ke kusa.
“Fasinjojin suna kan hanyarsu daga Bagega zuwa Anka lokacin da bam din ya fashe. Mutum daya ya mutu nan take, yayin da bakwai suka samu raunuka kuma yanzu haka suna samun kulawar likitoci,” in ji shi.
Yankin na fuskantar matsalar tsaro
Wannan sabon hari ya zo ne kasa da wata guda bayan wata makamanciyar fashewa da ta auku a wannan hanya, inda rahotanni suka nuna cewa mutum shida sun rasa rayukansu.
Lamarin ya kara jefa al’ummar yankin cikin fargaba tare da tayar da hankulan jama’a kan yadda matsalar tsaro ke kara kamari a wasu sassan jihar Zamfara..
‘Yan sandan Zamfara sun dauki mataki
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurin domin shawo kan matsalar.
Ya ce rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun dauki matakan gaggawa domin tabbatar da tsaron yankin da kuma dawo da zaman lafiya.
“Ana aiki tare da jami’an soji domin tantance halin da ake ciki, share hanyar daga duk wata barazana da kuma tabbatar da zaman lafiya ya dawo cikin gaggawa,” in ji Bello.

Source: Twitter
Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar wajen yakar ‘yan bindiga da masu aikata ta’addanci a Zamfara, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Ya bukaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri masu amfani domin taimakawa wajen dakile ayyukan miyagu.
An kashe yan bindiga 6 a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa jami’an tsaro sun dakile wani mummunan harin ‘yan bindiga a yankin karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: An shiga rudani kan yanayin da wani babban jami'in Kwastam ya rasu a Bauchi
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya bayyana cewa maharan sun zo ne da miyagun makamai.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi artabu mai zafi da maharan, inda suka kashe yan bindiga shida yayin d sauran suka ari na kare.
Asali: Legit.ng

