Filato: Gwamna Ya Kaɗu da Tsohon Mataimakin Gwamna da Ciyaman Suka Rasu
- Gwamnan Filato ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan tsohon mataimakin gwamna da tsohon ciyaman waɗanda suka rasu kwanan nan
- Caleb Manasseh Mutfwang ya bayyana tsofaffin jagororin biyu a matsayin mutane na gari, waɗanda suka yi wa al'umma hidima
- Gwamnan ya ce rasuwar manyan mutanen biyu ta shafi al'ummar jihar Filato gaba ɗaya, ba iyalansu kaɗai suka yi rashi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Gwamnan Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Sonni Tyoden.
Gwamna Mutfwang ya kuma yi jimamin mutuwar tsohon shugaban karamar hukumar Mangu, Baba Denis Lamu, wanda ya yi mulki na tsawon wa'adi biyu.

Asali: Twitter
A wata sanarwa da gwamnatin Filato ta wallafa a Facebook, Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana mutanen biyu a matsayin jarumai da suka yi wa al'umma hidima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya kaɗu da mutuwar shugabanni 2
Mutfwang ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan waɗannan fitattun ‘yan jihar domin jajanta musu bisa rasuwar ƴan uwansu.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakiyarsa, Ngo Josephine Piyo, da wasu manyan jami’an gwamnatin Filato zuwa gidajen mamatan a Jos, Pu
A lokacin ziyarar, ya miƙa ta’aziyyarsa cikin jimami tare da yabawa da irin rayuwa mai cike da sadaukarwa da kawo ci gaban al’umma da mamatan suka yi.
Mutfwang ya je alhini gidan Sonni Tyoden
A gidan marigayi tsohon mataimakin gwamna, Farfesa Tyoden, Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al'ummar Filato gaba ɗaya.
Ya ce:
“Na samu ganinsa a asibiti watan Nuwamba, gaskiya zuciyata ta karaya, na gode ma Allah saboda na ga an masa tiyata cikin nasara. Fatana zai warke amma Allah ya zabi abin da ya fi."

Asali: Facebook
Ya kara da cewa Farfesa Tyoden ya bar tarihi mai kyau a fannin ilimi da shugabanci, musamman lokacin da ya kasance Shugaban Jami’ar Jos.
Mutfwang ya kuma yaba da jajircewar matarsa da iyalansa wajen kula da shi lokacin jinyarsa, tare da godiya ga dukkan waɗanda suka tsaya masa har zuwa rasuwarsa.
Gwamna ya je ta'aziyyar tsohon ciyaman
A gidan tsohon ciyaman na Mangu, Baba Lamu da ke unguwar Jiyep Hwolshe a Jos, Gwamna Mutfwang ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen shugaba kuma dattijo nagari.
Ya kuma kira shi da gwarzon al’ummar Mwaghavul, wanda har yanzu ayyukan alherin da ya yi a karamar hukumar Mangu suna da tasiri.
"Baba Lamu ba kawai ɗan siyasa ba ne, mutum ne mai gina mutane da al’umma ne."
“Ina tuna yadda mahaifiyata ke yawan ambaton gadoji da ayyukan da ya yi, waɗanda har yanzu suna nan a tsaye, wannan shi ne jagoranci na gaskiya.”
- Caleb Mutfwang.
DSS ta hana gwamnatin Filato aiki?
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Filato ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa hukumar tsaron farin kaya ta hana ta ɗaukar matakai kan matsalar tsaro.
Gwamnatin Mutfwang ta bayyana raɗe-raɗin wanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a matsayar ƙarya mara tushe balle makama.
Ta yyana hukumar DSS a matsayin abokiyar aiki a yakin da take yi da matsalar rashin tsaron da ta addabi jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng