A ƙarshe, bayan Fargabar Halin da Yake Ciki, Mataimakin Gwamnan Taraba YA Dawo Gida

A ƙarshe, bayan Fargabar Halin da Yake Ciki, Mataimakin Gwamnan Taraba YA Dawo Gida

  • Mataimakin gwamnan Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya dawo Jalingo bayan kusan wata hudu yana jinya a Abuja da kasar Masar
  • An ce jirgin haya ne ya sauke shi a Filin Jirgin Saman Danbaba Suntai da misalin karfe 1:40 na rana, ba tare da sanar da ’yan jarida ba
  • Mai magana da yawun gwamna, Emmanuel Bello, ya tabbatar da dawowar Alkali, amma bai bayar da cikakken bayani kan lafiyarsa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Mataimakin gwamnan Taraba, Alhaji Aminu Alkali ya dawo Jalingo, babban birnin jihar.

Hakan ya biyo bayan shafe kusan wata hudu yana bai Jalingo wanda ya daga hankulan mutane.

A ƙarshe, mataimakin gwamna ya dawo Taraba
Bayan shafe wata 3 bai gida, mataimakin gwamnan Taraba ya dawo. Hoto: Agbu Kefas.
Asali: Facebook

Daily Trust ta gano cewa mataimakin gwamnan ya sauka a Filin Jirgin Sama na Danbaba Suntai a Jalingo, a jirgin haya da misalin 1:40 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda al'umma suka damu da rashin ganinsa

Wannan na zuwa ne bayan mutane sun fara shiga cikin damuwa a jihar Taraba kan rashin ganin Mataimakin Gwamna, Aminu Alkali na tsawon lokaci.

Ana fargabar Aminu Alkali bai bayyana a bainar jama'a ba har na tsawon kwanaki 90 kenan, kuma ba a yi wa jama'a bayani ba.

Rahotanni na cewa Alkari na fama da mummunan hawan jini kuma ana jinya a asibiti tun fiye da watanni biyu da suka wuce a Abuja, cewar Leadership.

Mataimakin gwamann Taraba ya dawo gida bayan wata 4 yana jinya
Fargaba ta kare bayan dawowar mataimakin gwamnan Taraba. Hoto: Agbu Kefas.
Asali: Twitter

APC ta bukaci sanin halin da yake ciki

Bayan haka, jam'iyyar APC mai adawa a Taraba ta bukaci Gwamna Agbu Kefas ya fito ya yi wa al'umma bayanin halin da mataimakinsa ke ciki.

APC ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ake surutu kan lafiyar mataimakin gwamnan da kuma wurin da yake kasancewar an jima ba a ji ɗuriyarsa ba.

Mataimakin gwamnan Taraba ya sauka Jalingo

Babu ’yan jarida a filin jirgin lokacin da ya iso domin ba a sanar da su da wuri ba cewa zai dawo garin.

An samu labarin cewa an fara kai mataimakin gwamnan Abuja domin jinya bisa wata rashin lafiya da ba a bayyana ba, daga baya aka kai shi Masar.

Wata majiya daga ofishinsa ta ce:

“An gaya mana cewa mataimakin gwamna ya dawo Jalingo amma babu wanda ya sanar da mu. Mun ji ne bayan ya isa birnin."

Mataimakin gwamnan bai da kakakin yada labarai, lamarin da ya sa ya zama da wuya a samu tabbacin dawowarsa a lokacin da ake hada rahoton.

Amma Mataimakin Gwamna kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa ta Intanet, Mr Emmanuel Bello, ya tabbatar da dawowar mataimakin gwamnan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Gwamna ya fadi halin da mataimakinsa ke ciki

Kun ji cewa Gwamnatin Taraba ta bayyana dalilin da ya sa aka daina ganin mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdullahi Alkali tun a watan Nuwambar 2024.

An ce rabon da a ga mataimakin gwamnan a cikin jama'a ko al'amuran gwamnatin Taraba da ya jawo ka-ce-na-ce.

Lamarin ya jefa masu ruwa da tsaki a Taraba a cikin damuwa, har ta kai ana tambayar halin da Aminu Alkali ya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.