Kwankwaso Ya Yi Magana kan 'Yan Majalisun NNPP da Suka Koma APC a Kano
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yunkurin fada da Kwankwasiyya a siyasa tamkar fada da bango ne da ba zai motsa ba
- Ya fadi hakan ne yayin da ya karbi wasu mutane sama da 100 da da suka bar APC zuwa NNPP daga karamar hukumar Takai a Kano
- Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi wadanda suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC da cewa kudi ne da kwadayi suka rinjaye su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi mangana kan 'yan siyasa masu sauya sheka bayan an zabe su.
Kwankwaso ya bayyana cewa duk wanda ke yunkurin fada da Kwankwasiyya yana bata lokaci ne, domin tafiyar ta riga ta kafa ginshiki mai karfi.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Kwankwaso ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya soki masu sauya sheka
Kwankwaso ya bayyana cewa wadanda suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC suna yi babban cin amana ga wadanda suka zabe su a karkashin tutar jam’iyyar NNPP.
Ya ce lamarin ya samo asali ne daga kwadayi da son zuciya, inda wasu ke karbar kudi daga manyan jam’iyyun gwamnati don canza sheka ba tare da tuntubar jama’a ba.
Madugun Kwankwasiyyar ya kara da cewa hakan babban cin amana ne kasancewar talakawa sun ki karbar taliya ko kudi, sun zabe su, amma su kuma suna karbar kudi suna sauya sheka.
Kwankwaso ya soki wasu ‘yan majalisar dokoki da suka bar NNPP zuwa APC, ciki har da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila.
'Fada da Kwankwasiyya fada ne da bango,' Kwankwaso
Jagoran NNPP ya jaddada cewa Kwankwasiyya ba jam’iyya ba ce kawai, tafiya ce ta sauyi da kyakkyawan shugabanci da ta shafi dubban matasa da dattawa a fadin Najeriya.
Bidiyon da Nasara Radio ta wallafa a Facebook ya yana cewa Kwankwaso ya ce duk mai fada da tafiyar Kwankwasiyya ba zai yi nasara ba, domin tamkar yana fada ne da bango.
Kwankwaso ya ce:
"Rigima da wannan tafiya ta Kwankwasiyya kuskure ne ba karami ba a wajen 'yan siyasa, wani ba zai gane ba sai ya yi yakin zai gane fada da bango abu ne mai wahala."
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da cewa tun a shekaru da dama ake samun darusa a siyasar Kano amma 'yan siyasa da dama sun gaza daukar darasi.

Asali: Facebook
Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi wasu 'yan NNPP da suka sauya sheka a Abuja.
Barau Jibrin ya bayyana cewa ya karbi mutanen ne daga dukkan shiyyoyin Kano uku tare da wasu mata 'yan siyasa a jihar.
Mutanen da suka sauya shekar sun ce sun dauki matakin ne domin nuna amincewa da goyon baya ga ayyukan da Sanata Barau ke yi.
Asali: Legit.ng