NNPP Ta Kai Wawura, Kwankwaso Ya Karbi 'Yan APC kusan 200 a Jihar Kano
- Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi sababbin mambobi 170 da suka sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP a ƙaramar hukumar Takai a Kano
- NNPP ta ce sauya sheƙar ya nuna yadda jam’iyyar ke ƙara samun karɓuwa daga tushe saboda adalci da gaskiyar shugabancinta
- Daga cikin dalilan da suka bayar barin jam'iyyarsu, wadanda suka bar APC sun ce sun gaji da rashin shugabanci nagari a jam'iyyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi sababbin yan jam'iyya 170 da suka sauya sheƙa daga APC a ƙaramar hukumar Takai da ke jihar Kano.
Wannan taron sauya sheƙa ya ja hankalin magoya baya da masoyan jam’iyyar NNPP, tare da nuna irin ƙarfin jam’iyyar a matakin ƙasa da ƙananan hukumomi.

Asali: Facebook
A sakon da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce NNPP na ta karbi yan APC, wanda ke nuna karin karfi tun daga tushe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jam’iyyar, wannan na ƙara tabbatar da yadda NNPP ke ƙara samun karɓuwa musamman saboda manufa da tsarin da gwamnatin Kano ke tafiya a kai.
Rabiu Kwankwaso ya karbi 'yan APC
Kwankwasiyya new media update ta wallafa a shafin Facebook cewa yayin da yake karɓar sababbin yan jam'iyya, Kwankwaso ya jinjinawa ƙudurinsu da jarumtar da suka nuna.
Sanata Kwakwaso ya kara da cewa jam'iyyar NNPP ta talaka ce, wanda aka samar saboda cicciba rayuwar al'umma.
A cikin jawabinsa, Sanata Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa da wannan sauyi, yana mai cewa:
"Muna maraba da ‘yan’uwa da suka fahimci gaskiya da adalcin NNPP. Wannan jam’iyya ce ta al’umma, kuma tare da goyon bayan kowa da kowa, za mu ci gaba da kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya."
Dalilin sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai jiga-jigan APC da suka shahara a siyasar karamar hukumar Takai.
Sun bayyana cewa amincewarsu da shugabancin Kwankwaso da hangen nesan NNPP, wanda yana daga cikin dalilansu na sauya sheka zuwa cikin jam'iyyar.

Asali: Facebook
A madadin sababbin 'yan jam'iyya da suka sauya sheka, Malam Sani Takai ya bayyana dalilinsu na barin APC.
Ya ce:
Mun fahimci cewa NNPP ita ce jam’iyyar da ke da gaskiya da burin kawo ci gaba ga talaka. Mun gaji da alkawuran banza da rashin shugabanci nagari a APC, don haka muka yanke shawarar haɗa kai da NNPP don gina ƙasa.
Shugaban APC ya aika sako ga Kwankwaso
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban APC Kano, Abdullahi Abbas, ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin NNPP ta gaza, yana mai zargin ta da cutar jama'a.
A wani taron magoya bayan jam’iyyar da aka gudanar a Kano, Abbas ya yi ƙarin bayani game da yadda, a cewarsa, gwamnatin Kano ke kuntatawa jama'a tun bayan hawanta mulki.
Ya yi ikirarin cewa ba za su saurara wa 'yan Kwankwasiyya a babban zabe mai zuwa ba, har ya yi gargadin cewa ko da tsiya, ko da tsiya tsiya, sai APC ta kwace mulki daga NNPP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng