Gwamna Uba Sani Ya Koka kan Gagarumar Matsalar da Ta Tunkaro Matasan Arewa
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwarsa kan yadda matasan Arewacin Najeriya suke ta'ammali da kayan sanya maye
- Uba ya koka kan yadda matasan musamman na Arewa maso Yamma suka rungumi ɗabi'ar amfani da magunguna irinsu codeine da tramadol
- Gwamnan ya nuna cewa hakan babbar barazana ce ga lafiyar jama'a, zaman lafiya da tsaron yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana damuwa kan yawaitar amfani da magungunan 'opioid' ba bisa ƙa’ida ba a yankin Arewacin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya nuna damuwa kan amfani da magugunan ne musamman Tramadol da Codeine, a tsakanin matasa a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Asali: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da ƙungiyar PSN reshen jihar Kaduna ta shirya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya liyafar ne domin murnar nasarar zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar na ƙasa, Pharm. Ayuba Ibrahim, da mataimakiyar shugaba (yankin Arewa), Pharm. Aisha Isyaku, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Uɓa Sani ya damu kan shan ƙwayoyi a Arewa
Uba Sani ya samu wakilcin shugaban hukumar KADBUSA, Joseph O. Ike, a wajen liyafar.
Gwamna Uba Sani ya ambato binciken UNODC na shekarar 2018 wanda ya nuna cewa mutum ɗaya cikin bakwai a Najeriya yana amfani da miyagun ƙwayoyi, kuma alƙaluman sun fi yawa a yankin Arewa maso Yamma.
“A nan Arewa maso Yamma, muna fuskantar yawaitar amfani da magungunan opioid kamar Tramadol da Codeine fiye da ƙima."
“Abin damuwa ne matuƙa, saboda muna da masaniyar cewa mutum ɗaya cikin biyar daga cikin masu amfani da irin waɗannan magunguna sukan faɗa cikin dogon shaye-shaye."
"Hakan yana haifar da barazana ba kawai ga lafiyar jama’a ba, har da tsaro da ci gaban yankin baki ɗaya.”
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya yabi shugabannin PSN
Gwamna Uba Sani ya kuma yaba da sabon shugabancin da ƙungiyar PSN ta samu a matakin ƙasa ƙarkashin Pharm. Ayuba Ibrahim a matsayin shugaba da Pharm. Aisha Tukur Isyaku a matsayin mataimakiyar shugaba (yankin Arewa).

Asali: Facebook
Ya ce yana da tabbacin cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnati da masana harkar magani zai ƙara ƙarfi domin kawo ci gaba mai ɗorewa a fannin kiwon lafiya a jihar Kaduna da Najeriya gaba ɗaya.
“Fahimtarku wajen bayar da magunguna, ba da shawara ga marasa lafiya, samar da bayanai game da magunguna, na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burinmu na samar da lafiya mai inganci kuma mai sauƙin samu ga kowa da kowa a jihar Kaduna."
- Gwamna Uba Sani
Gwamnatin Uba Sani ta ƙwace filaye
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta ba da umarnin ƙwace wasu filaye da gidaje da aka ba da ba bisa ƙa'ida a gwamnatin da ta gabata.
Filaye da gidajen da za a ƙwacen dai suna a makarantun Alhuda-Huda da ke Zariyada Queen Amina College da ke garin Kaduna.
Gwamnatin ta yi bayanin cewa an kwace filayen ne da nufin dawo da su don amfanin jama’a da kuma kare makarantun da kuma samun damar faɗaɗa su.
Asali: Legit.ng