"Karyarku Ta Sha Karya," Tinubu Ya Ɗauki Zafi kan Masu Yunkurin Tarwatsa Najeriya

"Karyarku Ta Sha Karya," Tinubu Ya Ɗauki Zafi kan Masu Yunkurin Tarwatsa Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa Najeriya ba za ta bari masu yunkurun tarwatsa ta su samu galaba da
  • Mai girma Tinubu ya yi gargaɗi mai zafi ga duk masu hannu a shirin ruguza Najeriya a gida ko daga ƙasashen ketare
  • Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da kayan aiki ga dakarun sojoji domin kawo karshen duk wata matsalar tsaron jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi gargaɗi mai zafi ga wadanda ya bayyana a matsayin “masu haɗin baki a cikin gida ko daga waje” da ke kokarin tarwatsa Najeriya.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga dakarun sojin Najeriya da ke yaki da ta'addanci da miyagun laifuffuka a jihar Katsina.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya ja kunnen masu yunƙurin tarwatsa Najeriya a ziyarar da ya kai Katsina Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya gargaɗi masu shirin tarwatsa Najeriya

Da yake jawabi ga sojojin da suka tarbe shi a ziyarar kwanaki biyu da ya fara a Katsina ranar Juma'a, Bola Tinubu ya ce Najeriya ba za ta saduda ba.

Shugaban ƙasa ya ce:

"Ga duk waɗanda ke ƙoƙarin tarwatsa mana kasa, a nan gida suke ko daga ƙasashen ƙetare, ku ƙasa kunne su ji, Najeriya ba za ta sunkuyar da kai ba. Ba ga tsoro, ta’addanci ko cin amana ba."

Shugaban kasa Tinubu ya jinjinawa sojoji

Shugaba Tinubu ya kuma yabawa jarumtakar dakarun soji, yana mai kiransu da, “garkuwar Najeriya” kuma “masu kare dimokuraɗiyya.”

"Ku ne cikakkun jarumai mata da maza da ke tsaye tsakanin al’umma da ƴan tayar da ƙayar baya.

"Kowane wuri da kuka tsare, kowanne dan ta’adda da kuka kawar, kowace unguwa da kuka tsare, kuna kara tabbatar da nasara ga adalci, ‘yanci, da goben yaranmu.”

- Bola Tinubu.

Dakarun sojoji.
Shugaba Tinubu ya yi wa sojojin albishir na inganta walwalarsu Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa tana ci gaba da samar isassun kayan aiki da jin dadin dakarun sojojin Najeriya.

“Muna samar muku da manyan makamai, sahihin bayanan leƙen asiri da ƙarin tallafin kayan aiki, ba kawai domin kare ƙasa ba, har ma da kawar da kowane makiyi.”

Tanadin da Tinubu ya yi wa sojoji

Tinubu ya kuma tabbatar wa dakarun cewa jin dadin su da na iyalansu yana da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa.

“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa iyalanku suna cikin tsaro, ana biyan hakkokinku a kan lokaci, kuna samun kulawa ta lafiya, kuma ana mutunta martabarku," in ji shi.

Tinubu ya ƙara da cewa akwai shirye-shiryen gidaje, tallafin iyali, inshora da ƙarin albashi da aka riga aka fara aiwatarwa domin walwalar sojoji da iyalansu.

Tinubu ya ɗauki mataki kan kisan fararen hula

A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya ɗauki zafi kan kashe-kashen rayukan ƴan kasa da ke ƙaruwa a jihohin Filato, Borno da Benuwai.

Mai girma shugaban kasa ya umarci a sauya dabarun tsaro nan take da kuma daukar matakan gaggawa don kawo karshen tashin hankalun da ke faruwa.

Shugaban ya gana da hafsoshin tsaro na tsawon sa’o’i biyu a fadar gwamnati, inda ya ce ya zama dole a dakatar da kashe fararen hula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262