Za a Kashe Dala Miliyan 158 domin Noma da Yaki da Talauci a Jihohin Arewa 9

Za a Kashe Dala Miliyan 158 domin Noma da Yaki da Talauci a Jihohin Arewa 9

  • Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kaddamar da shirin VCN mai darajar dala miliyan 158.15 domin bunkasa noma a Arewa
  • Shirin zai tallafa wa manoma a jihohi tara na Arewa, ciki har da: Kano, Sokoto, Katsina da Borno cikin tsawon shekaru takwas masu zuwa
  • Ana sa ran shirin zai rage talauci, inganta samar da abinci da karfafa lafiyar al’umma a yankunan karkara da suka fi fuskantar matsaloli

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A wani gagarumin mataki na bunkasa harkar noma a Najeriya, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na VCN.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kaddamar da shirin ne a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Arewa
Za a bunkasa noma a jihohin Arewa 9. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda shirin zai gudana ne a cikin wani sako da Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin ya tanadi kudin da ya kai Dala miliyan 158.15 kuma za a aiwatar da shi kai tsaye a jihohin Arewa tara cikin shekaru takwas.

Kashim Shettima ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne sakamakon rokon da ya yi ga hukumar IFAD a Rome a shekarar 2023 domin fadada ayyukanta a Najeriya.

Jihohin Arewa da za su ci gajiyar shirin

A cewar sanarwar, jihohin da za su ci gajiyar shirin sun hada da Borno, Bauchi, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto, Yobe da Zamfara.

Za a mayar da hankali kan karfafa darajar amfanin gona da samar da damar tattali ga manoma da masu ruwa da tsaki a harkar noma, tare da tabbatar da dorewar bunkasar abinci.

An tsara shirin ne domin warware matsalolin da masu noman abinci ke fuskanta tare da tallafa musu da dabaru da kayayyakin noma na zamani.

Hadin gwiwar IFAD, AFD da Najeriya

Shirin na VCN na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar IFAD ta duniya, hukumar bunkasa kasashe ta Faransa (AFD) da gwamnatin Najeriya.

An tabbatar da shirin tun daga ranar 21 ga Maris, 2024, kuma za a aiwatar da shi ne bisa tsarin kawo cigaba na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Shettima
Shettima ya ce za a yaki talauci a Arewa ta hanyar noma. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Wannan hadin gwiwar na nuni da yadda Najeriya ke kokarin hada kai da hukumomi da kasashe domin cimma burin wadatar abinci da tsare lafiyar al’umma.

Za a rage talauci a Arewa, a karfafa al’umma

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jaddada cewa shirin zai taimaka matuka wajen rage talauci, inganta lafiyar al’umma da tabbatar da dorewar arzikin yankunan karkara.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da hada gwiwa da sauran abokan hulda don ganin an rage nauyin da ke kan al’umma da manoma a Arewa.

Legit ta tattauna da manomi a Bauchi

Wani manomi a garin Nahuta da ke karamar hukumar Sade ta jihar Bauchi ya ce za su yi farin ciki idan suka samu tallafin.

Malam Nura ya bayyanawa Legit cewa:

"Muna da wurin noman rani da damuna amma ba kowa yake yin noman rani ba.
"Muna fatan gwamnati za ta shigo irin wuraren mu domin ba mu tallafi mu rika noma sosai a rani."

Masu casar shinkafa sun koka da farashi

A wani rahoton, kun ji cewa masu casar shinkafa sun koka kan yadda farashin abinci ke karyewa a Najeriya.

Sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta sake dubi kan shigo da abinci daga ketare domin bunkasa harkar noma a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa masana'antun da suke casar shinkafa a Arewacin Najeriya sun fara rufewa saboda karyewar farashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng