"Mutum mai Gaskiya da Rikon Amana," Gwamna Radda Ya Sha Ruwan Yabo daga Bakin Tinubu

"Mutum mai Gaskiya da Rikon Amana," Gwamna Radda Ya Sha Ruwan Yabo daga Bakin Tinubu

  • Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sha ruwan yabo daga bakin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a ziyarar da ya kai jihar
  • Tinubu ya bayyana Dikko Raɗɗa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, kuma mai sadaukarwa da jajircewa wajen gudanar da mulki
  • Ya ce nasarorin da gwamnan ya samu a shekara biyu abin a yaba ne kuma gwamnatin tarayya tana tare da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, bisa gaskiya, rikon amana da jajircewarsa wajen gudanar da mulki.

Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya fara a jihar tun ranar Juma’a, inda ya kaddamar da Cibiyar Inganta Aikin Noma ta Katsina.

Dikko Radda.
Shugaba Tinubu ya gamsu da salon mulkin Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Tinubu ya kira Malam Dikko Raɗɗa da mutum mai gaskiya da rikon amana, yana mai cewa gwamnatin tarayya na tare da shi, kamar yadda Premium Times ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa

Shugaba Tinubu ya ce:

"Ci gaban da ka samar a cikin shekara biyu musamman a fannonin noma, ababen more rayuwa da walwalar jama’a, abin yabo ne. Kai gwamna ne mai gaskiya, rikon amana da sadaukarwa."

Bola Tinubu kuma ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa gwamnatin tarayya na tare da su, za ta ci gaba da tallafawa Gwamna Dikko Radda don ƙara nunka ayyukan da yake yi.

Shugaban ya bukaci sauran gwamnonin jihohi su mai da hankali wajen aiwatar da ingantattun ayyuka da za su tallafi rayuwar al’umma kai tsaye, maimakon damuwa da masu sukar gwamnati daga gefe.

Daga cikin ayyukan da shugaban ƙasa ya kaddamar a ziyarar, akwai titin Ajiwa-Ruwan Godiya mai tsawon kilomita 24 da aka kammala cikin watanni 18 kacal.

Me Tinubu ya ce game da rashin tsaro?

Game da kalubalen tsaro, shugaban ƙasa ya ce:

“Fatanmu a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Na san kuna fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, amma (Dikko Raɗɗa) ka nuna jajircewa da kwarin gwiwa wajen ciyar da jihar gaba.
"Gwamnatin Tarayya ba za ta barka kai kaɗai ba, muna tare da kai."

Abubuwan da ke rura wutar matsalar tsaro

Shugaba Tinubu ya bayyana yunwa da talauci a matsayin manyan barazana ga zaman lafiya a Najeriya, yana mai cewa tattalin arzikin ƙasar na kan tafarkin da ya dace.

Ya jadadda cewa gwamnatinsa ta tashi tsaye domin kawar da yunwa da fatara kuma ta duƙufa wajen samar da isasshen abinci ga al'umma, Channels tv ta rahoto.

Shugaba Tinubu.
Tinubu ya ce gwamnatinsa na tare da Dikko Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Twitter

A karshe, ya ƙara da jinjinawa Gwamna Radda bisa nasarorin da ya samu a bangaren noma, ilimi, kiwon lafiya da gine-gine, yana mai cewa:

“Na saurari bayanan da ka yi, a cikin rabin wa’adinka, ka cimma abubuwan da yawa. Gaskiyarka da ƙwazonka abin yabo ne. Kai dan kishin kasa ne, ɗan jihar Katsina kuma mai hangen nesa.”

Tinubu ya ɗauki zafi kan masu rura ta'addanci

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya gargaɗi waɗanda ya kira masu shirin ruguza Najeriya, yana mai cewa Najeriya ta fi ƙarfinsu.

Bola Tinubu ya ce Najeriya ba za ta durƙusa wa masu mummunar manufa ga ƴan ƙasarta ba kuma za ta yi duk mai yiwuwa ta ga bayansu.

Mai girma shugaban ƙasa ya yi wannan kalamai ne yayin da ya kai ziyara ta kwanaki biyu jihar Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da aka rasa zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262