'Yaudara ce,' Atiku Ya Soki Matakin Tinubu kan Hana Shigo da Kayan Waje a Najeriya
- Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu da ya sayar da motarsa kirar Escalade, ya koma amfani da motar da aka kera a Najeriya
- Ya kuma nemi shugaban ƙasa ya daina zuwa ƙasashen waje don duba lafiya, ya koma amfani da asibitocin Najeriya irin su LUTH da UCH
- Atiku na wannan batu ne a kan sabon umarnin da shugaban kasa ya bayar na haramta shigo da kayan da za a iya sarrafa wa a Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana sabon taken gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kihsin kasa a matsayin sabuwar farfaganda.
Ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin yaudarar jama'a da jefa rudani a zukatansu, yayin da shugaban kasa ke sha'aninsa a kasashen waje.

Asali: Facebook
Kalubalen Atiku Abubakar ga Bola Tinubu
Leadership News ta wallafa cewa, Atiku ya kalubalanci shugaban ƙasa da ya nuna kishin kasa ta hanyar amfani da sabuwar manufarsa ta hana shigo da kaya da za a iya sarrafawa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shawarce shi ya sayar da motocin da ya ke hawa, ya koma amfani da motar da aka kera a Najeriya kamar na kamfanin Innoson ko Nord.
Atiku ya ce mutane sun gaji da surutu
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun gaji da umarnin gwamnati, kuma ba a katabus.
Ya ce idan har gwamnatin Tinubu tana da niyyar ƙarfafa masana’antun cikin gida, to ya kamata a fara daga manyan jami’an gwamnati.

Asali: Facebook
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗar jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce:
“Muna kalubalantar Shugaba Tinubu da ya daina surutu, ya sayar da motar Escalade ɗinsa ya koma amfani da Innoson ko kowace mota da aka kera a Najeriya.”
Ya kuma ƙara da cewa:
“Mu kuma ga ministocinsa — waɗanda ke sha’awar Rolls Royce — su gwada zama cikin motar da aka kera a Najeriya. Ko kuwa kishin kasa za ta tsaya ne kawai a kan talakawa?”
Atiku ya shawarci shugaba Tinubu
Atiku ya shawarci shugaban ƙasa da ya daina yawo a biranen Paris da London idan da gaske yana da kishin ƙasa.
Ya ce:
“Idan har shugaban ƙasa yana da kishin ƙasa da gaske, to yawon buɗe ido na gaba da zai je ya kasance a Obudu Cattle Ranch, ko Yankari Game Reserve, ko Erin Ijesha Waterfalls. Najeriya ƙasa ce mai kyau — sai dai idan shugaban ƙasa yana da wani tunani na daban.”
Ya ƙara da cewa:
“Wannan halin na fita waje domin duba lafiya yayin da ake faɗin a dogara da kai ya kamata ya tsaya. Muna buƙatar ganin Shugaba Tinubu, wanda ke ɗaukar kansa a matsayin dan kishin kasa, ya rika duba lafiyarsa a LUTH, Asibitin Ƙasa na Abuja, UCH Ibadan ko kuma babban asibitin da aka gina a Uyo na Akwa Ibom da kuɗi N41bn.”
Masani ya shawarci gwamnatin Tinubu
Dr. AbdulNasir Turawa Yola, Masanin tattalin arziki ne a Arewacin Najeriya, ya shaidawa majiyar Legit cewa akwai hanyoyi da dama na inganta tattalin arzikin kasa.
Ya ce:
"Wannan mataki ne mai kyau, amma aiwatar da shi yanzu zai cutar da jama'a."
"Idan ana son matakin ya haifar da da mai ido, sai an gyara yadda ake tafiyar da masana'antun ƙasar nan baki daya."
Ya kara da cewa masana'antun ƙasar nan na bukatar abubuwa da dama domin iya tafiyar da aikinsu, daga ciki akai tabbatar da wutar lantarki.
Atiku ya ƙaryata shirin shiga APC
A wani labarin, kun ji tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wazirin Adamawa ya tabbatar da cewa yana nan daram a jam’iyyar PDP, inda ya ce haɗakar siyasa da yake jagoranta za ta yi nasarar kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Atiku ya yi wannan furuci ne lokacin da ya karɓi baƙuncin mata ƴan majalisar amintattu ta jam’iyyar PDP (BoT), waɗanda suka kai masa ziyara don jaddada goyon bayansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng