Bayan Gwamnan Delta Ya Dawo APC, Takwaransa na PDP Ya Fadi Matsayarsa

Bayan Gwamnan Delta Ya Dawo APC, Takwaransa na PDP Ya Fadi Matsayarsa

  • Kwamishinan yada labarai na jihar Akwa Ibom ya musanta rade-radin cewa Gwamna Umo Eno na shirin ficewa daga PDP zuwa APC
  • Ya ce goyon bayan Eno ga Shugaba Bola Tinubu da Godswill Akpabio dabarar bunkasa hadin gwiwa ce domin amfanar da jama'ar jihar
  • Umanah ya bayyana cewa hadin gwiwar gwamnati ta kawo sauyi kamar Ibom Seaport da gyaran muhalli da ci gaban al'umma baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Kwamishinan yada labarai na jihar Akwa Ibom, Rt. Hon. Aniekan Umanah ya yi magana kan rade-radin Gwamna Umo Eno zai koma APC.

Umanah ya musanta jita-jitar cewa Gwamna Eno na PDP na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna ya ƙaryata shirin komawa APC
Gwamna Umo Eno ya ƙaryata labarin komawa APC daga PDP. Hoto: Pastor Umo Eno, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Gwamna ya musanta shirin komawa APC daga PDP

Wadannan jita-jita sun biyo bayan yawan kusancin Gwamna Eno da gwamnatin tarayya da kuma goyon bayansa ga Bola Tinubu, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Umanah, gwamnan na goyon bayan Tinubu ne saboda neman hadin guiwa da gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ce:

"Goyon bayan Gwamna Umo Eno ga Shugaba Tinubu da Sanata Akpabio wata dabara ce ta bunkasa hadin gwiwa don ci gaban jihar."
"Goyon bayan shugaban kasa da manyan jami’an tarayya ba batun jam’iyya bane, dabara ce ta ci gaba."
"Wannan sabuwar hadin gwiwar ta fara haifar da gagarumar riba kamar 'Ibom Deep Seaport' da gyaran muhalli da wasu muhimman ayyuka."

Umanah ya bayyana goyon bayan Eno ga Shugaba Tinubu da Sanata Godswill Akpabio a matsayin mataki mai hangen nesa da nufin ci gaban jihar Akwa Ibom.

Gwamna ya yi magana kan rade-radin zai bar PDP zuwa APC
Gwamna Umo Eno ya musanta labarin barin PDP zuwa APC. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Tinubu ya yabawa gwamnan PDP kan ayyukan alheri

Umanah ya ce, Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da Godswill Akpabio sun yaba da ci gaban da Gwamna Eno ke samarwa a kowane lokaci.

Kwamishinan ya yaba da nasarorin Mai girma Eno a cikin watanni 23 da suka gabata, yana mai cewa yana bin tsarin mulki mai inganci.

Ya ce wannan tsari yana mayar da hankali kan noma, ci gaban karkara, ababen more rayuwa, tsaro, ilimi da kuma tallafin jin kai ga jama'a, Premium Times ta ruwaito.

"Tun daga 29 ga Mayu, 2023, Gwamna ya fara aiki da gaggawa. Ba ya alkawari kawai, yana cika su da aiki a fadin jihar."

- Umanah

Ya kara da cewa ana gina sabbin makarantu na zamani da asibitoci a kauyuka da birane tare da shirye-shiryen tallafawa jama'a masu tasiri sosai.

Gwamnan Delta ya bar PDP zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa bayan yada jita-jita, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gwamna Oborevwori ya sanar da haka ne a wata ganawar sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, inda manyan shugabannin APC suka karɓe shi hannu biyu biyu.

Sauyin jam’iyyar ya zo daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a siyasar jihar Delta, tare da shirye-shiryen goyon bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.