Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Kamu ana tsaka da Batun Sauya Sheƙar Gwamnan Delta

Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Kamu ana tsaka da Batun Sauya Sheƙar Gwamnan Delta

  • Kwanaki kalilan bayan ta rasa gwamnan jihar Delta da manyan ƙusoshinta, jam'iyyar PDP ta yi babban kamu a jihar Enugu
  • KakakinLP reshen jihar Enugu da tsohon kwamishina kuma jagora a kwamitin kamfen Obi/Datti 2023 sun sauya sheƙa zuwa PDP
  • Shugaban PDP na Enugu, Martin Chukwunwike ya ce Gwamna Peter Mbah ya ba su umarnin dawo da tsofaffin ƴaƴan da suka bar su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu - Mai nagana da yawun jam'iyyar LP na jihar Enugu, Mista Titus Odo, ya sauya sheka zuwa PDP a ranar Laraba, 30 ga watan Afrilu, 2025.

Odo ya koma PDP tare da tsohon Kwamishinan Harkokin Sarauta na jihar, Prince Emeka Mamah, wanda ya kasance Jagora a Kwamitin Kamfen Shugaban Kasa na Peter Obi a zaben 2023.

Emeka Mamah.
Kakakin LP da tsohon kwamishina sun sauya sheka zuwa PDP Hoto: Prime Minister Orf Enugu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa tun farko manyan ƴan siyasar guda biyu sun fice daga PDP zuwa jam’iyyar LP a kakar zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyr PDP ta yi babban kamu a Enugu

Da yake karbarsu a sakatariyar jam’iyyar ta jihar, Shugaban PDP na Enugu, Dakta Martin Chukwunwike, ya bayyana farin cikinsa kan matakin da suka ɗauka na dawowa gida.

Ya bayyana cewa Gwamna Peter Mbah ne ya umurci shugabannin PDP da su yi duk mai yiwuwa domin dawo da ‘ya’yan jam’iyyar da suka bar ta saboda dalilai daban-daban.

“Mun yi farin ciki da kuka dawo cikinmu, kuma Allah na tare da jam’iyyarmu, ta shirya tunkarar zaben 2027," in ji shi.

Martin Chukwunwike ya kuma bukaci hadin kai a cikin jam’iyyar PDP domin gyara tsarin jam'iyyar da shirin fuskantar zaben 2027.

Dalilan jiga-jigan 2 na komawa PDP

A lokacin da aka gabatar da su ga shugaban PDP na Enugu, Titus Odo ya bayyana farin cikinsa na dawowa jam'iyyar PDP, yana mai cewa ayyukan alherin Gwamna Mbah ne suka ja ra’ayinsa.

A rahoton Vanguard, Mista Odo ya ce:

“Ina farin cikin sanar da ku cewa na dawo gida. Na dawo ne saboda manyan ayyukan ci gaba da Gwamna Mbah ke gudanarwa, kuma ina ƙara yaba masa
“Dalili na biyu da ya sa na dawo PDP shi ne sauya sheƙar tsohon ubangidana, wanda ya tsaya takarar gwamna a Enugu karkashin LP a 2023, Dokta Chijioke Edeoga.
“Dalili na uku shi ne yadda shugaban ƙaramar hukumar Igboeze ta Arewa, Mista Uchenna Ogara, ya kamo hanyar canza yankinmu zuwa gari na zamani."
Gwamna Mbah.
Jam'iyar PDP ta fara sasantawa da tsofaffin ƴaƴanta a Enugu Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

A nasa bangaren, Yarima Emeka Mamah ya gode wa shugabannin PDP a Igboeze ta Arewa, shiyyar Enugu ta Arewa da kuma reshen jam’iyyar na jihar saboda karbarsa hannu biyu.

Ya yabawa Gwamna Mbah saboda bude kofar sulhu ga wadanda suka bar jam’iyyar a baya, yana mai cewa, “Ni kai na na gamsu da kokarin da gwamnanmu ke yi.”

PDP za ta maka gwamnan Delta a kotu

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi watsi da sauya sheƙar gwamnan jihar Delta da wasu jiga-jigai zuwa APC mai mulkin ƙasa.

Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya ce ba za su kyale wannan lamarin haka nan ba, za su kai ƙara gaban kotu.

Ya ce tuni PDP ta ba da umarnin fara shirye-shiryen gurfanar da Gwamna Sheriff Oborevwori da sauran waɗanda suka bi shi zuwa APC a gaban ƙuliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262