Atiku ko Obi?: El Rufa'i Ya Yi Magana kan Tsayar da 'Dan Takaran 'Yan Adawa a 2027
- Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa hadakar jam’iyyun adawa ba ta bukatar tallafin gwamnoni
- El-Rufai ya ce a yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne gina dandalin da za a aminta da shi, ba zaben ‘yan takara ba
- Haka zalika ya musanta jita-jitar cewa suna shirin hadewa da PDP, yana mai cewa jam’iyyar ba ta da tasiri a yanzu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce hadakar jam’iyyun adawa da ke kara karfi a kasar nan ba ta bukatar goyon bayan gwamnoni.
El-Rufai ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kano, yana mai cewa burin kawancen shi ne jan hankalin masu kada kuri’a kai tsaye.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Nasir El-Rufai ya ce lokaci bai yi ba da za a fara tattauna sunayen ‘yan takara a tafiyar 'yan adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Maganar fitar da 'dan takarar 'yan adawa
Lokacin da aka tambaye shi ko akwai yiyuwar a tsayar da ‘yan takara kamar Atiku Abubakar ko Peter Obi, El-Rufai ya ce yanzu ba lokacin hakan ba ne.
Tsohon gwamnan ya ce:
“A yanzu burinmu ba zaben ‘yan takara ba ne, sai mun fara gina dandali mai karfi.
"Mun shaidawa duk masu son takara cewa su dakatar da muradinsu na dan lokaci, su zo mu hada kai a matsayin ‘yan uwan juna,”
Ya ce duk da suna maraba da wadanda ke da farin jini, amma za a fi mayar da hankali kan amincewar jama’a da kuma gina ingantacciyar mafita ga kasa.
El-Rufa'i ya kara da cewa:
“A nan gaba idan muka kammala hada kai a karkashin SDP, za mu fara batun takara.
"Amma yanzu muna kan matakin daidaita kawunan juna da gina dandalin da za a dogara da shi ne,”
“Ba mu da niyyar hadewa da PDP,” El-Rufa'i
El-Rufai ya bayyana cewa tun farko ba su da niyyar yin hadaka da PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta riga ta gagara tsayawa da kafafunta.
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa El-Rufa'i ya ce:
“Mun fada tun farko cewa PDP ba ta cikin lissafinmu. Jam’iyyar da ta kusa rushewa ba za ta iya zama mafita ba."
Ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su fahimci cewa kasar na cikin halin kunci mai barazana ga wanzuwar ta.
"Muna kokarin hada kai a SDP,' – El-Rufai
A karshe, El-Rufai ya bayyana cewa ana kokarin hada dukkan 'yan adawa a karkashin jam’iyyar SDP.
Ya kuma bayyana cewa ba hadakar jam’iyyu ake nema ba, domin sun san yadda hakan ke da wahala da tsawo.

Asali: Facebook
Ganduje: 'Wasu 'yan siyasa za su koma APC'
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce wasu gwamnonin PDP za su koma APC.
Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi a jihar Delta domin karbar gwamnan jihar da ya sauya sheka.
Shugaban jam'iyyar ya ce ayyukan da Bola Tinubu ke shimfidawa a Najeriya ne suke sanya 'yan siyasa komawa APC a fadin kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng