2027: El Rufai Ya Ziyarci Sanusi II, Ya Faɗa Masa Gaskiyar Dalilin Komawarsa SDP
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai ziyara ga Muhammadu Sanusi II a Kano inda ya ce jihar na da muhimmanci a tsarin siyasa
- Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP domin gina sabon tafarki na siyasa ba tare da uban-gida ba
- Ya ce duk da goyon bayan mulkin Kudu a baya, yanzu yana fifita cancanta da kwarewa fiye da kabilanci wajen zaben shugabanni a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano.
El-Rufai ya kai ziyarar a jiya Litinin 28 ga watan Afrilun 2025 a fadar basaraken da ke birnin Kano.

Asali: Facebook
El-Rufai ya gana da Sanusi II a Kano
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanusi II Dynasty ya wallafa a shafin Facebook a jiya Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin ziyarar, El-Rufai ya ce Kano na da matukar muhimmanci a kowanne tsarin siyasa saboda yawan masu kada kuri'a.
El-Rufai, wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP, ya ce Najeriya na bukatar sahihin tsarin siyasa domin ceto kasar.
Ya ce:
"Kano na da matukar muhimmanci a kowanne tsarin siyasa saboda yawan masu kada kuri'a.
"Bayan shiga SDP, ya zama dole in zo in gana da masu ruwa da tsaki a nan, da jaddada muhimmancin Kano a siyasa.
"Shekaru 12 da suka gabata, mun hade jam'iyyu guda uku muka kafa APC muka kayar da shugaban kasa mai ci.
"Amma yanzu burin ya sha bamban. Muna hada ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban a karkashin SDP domin samar da ingantaccen tafarki."
Tsohon gwamnan ya kara da cewa ya shiga SDP ne domin taimakawa wajen gina sabuwar siyasa mai zaman kanta ba tare da siyasar uban-gida ba.

Asali: Facebook
El-Rufai ya fadi abin da ya lalata APC
El-Rufai ya ce siyasar uban-gida da rikicewar jam’iyyun ne suka lalata APC da PDP, yana mai cewa Najeriya na bukatar jam'iyya mai adalci da dimokuradiyya.
Ya kara da cewa:
"Mun ga yadda siyasar uban-gida ta lalata PDP kuma yanzu tana lalata APC. Mutanen Najeriya sun cancanci jam’iyya mai adalci."
El-Rufai ya kara da cewa ko da yake ya taba goyon bayan tsarin karba-karba na mulki tsakanin Kudu da Arewa, yanzu cancanta yafi muhimmanci.
Ya ce halin da Najeriya ke ciki yanzu yana bukatar shugabanci mai nagarta fiye da fifita kabilanci ko asalin yankin shugabanni.
Kwankwaso ya ci karo da El-Rufai a Abuja
Kun ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya hadu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja yayin da ake ta rade-radin sauya sheƙar jagoran NNPP.
An ce an gano El-Rufai da ɗansa suna gaisawa da Kwankwaso bayan idar da sallar Juma’a a wani masallaci a Abuja.
Majiyoyi sun ce duk da cewa a masallaci suka hadu, ganin su tare ya dauki hankali da ƙara ƙarfafa jita-jitar cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng