Tafiyar El Rufa'i Ta Girgiza APC da Sauran Jam'iyyu, Tarin Mutane Sun Koma SDP a Gombe

Tafiyar El Rufa'i Ta Girgiza APC da Sauran Jam'iyyu, Tarin Mutane Sun Koma SDP a Gombe

  • Fiye da mutane 500 daga ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe sun sauya sheƙa daga jam’iyyun APC, PDP da NNPP zuwa jam'iyyar SDP
  • Masu sauya sheƙar sun bayyana tsofaffin jam’iyyunsu a matsayin "Jam’iyyu marasa inganci" tare da jinjina wa SDP a matsayin mafita ga Najeriya da Gombe
  • Shugabannin SDP a matakin jiha da ƙaramar hukuma sun tarbi sababbin mambobin tare da kiran da a ƙara ƙaimi wajen yaɗa manufofin jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - A wani abu da ke kama da girgizar siyasa a jihar Gombe, fiye da mutane 500 daga gundumar Kalshingi a karamar hukumar Akko sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar SDP.

Masu sauya sheƙar sun haɗa da matasa, mata da shugabannin al’umma, inda suka zargi jam’iyyun da suka bari da gazawa da cin amanar jama'a.

SDP Gombe
Daruruwan mutane sun koma SDP a Gombe. Hoto: SDP National Update
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda mutanen suka sauya sheka ne a cikin wani sako da SDP ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, rahoton da mai ba wa shugaban SDP na jihar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Abdulkadir Kumo ya fitar ya tabbatar da sauya shekar mutanen.

Maganar masu sauya sheka zuwa SDP

A wajen taron maraba da sababbin mambobin, shugaban SDP na ƙaramar hukumar Akko, Usman Muhammad, ya miƙa mambobin ga shugaban riko na SDP a jihar, Adamu Abubakar Modibbo.

Masu sauya sheƙar sun bayyana tsofaffin jam’iyyunsu da suka bari a matsayin "Marasa tsari" da suka gaza cika alkawuran da suka ɗauka.

SDP ta yi alkawarin jagoranci na gaskiya

Kwamared Modibbo ya yi maraba da sababbin mambobin inda ya bayyana cewa jam’iyyar SDP za ta basu damar taka rawa da samun wakilci na gaskiya.

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a faɗaɗa yaɗa manufofin SDP zuwa kowane gida a cikin ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

SDP Kaduna
"yan SDP yayin wani taro a Kaduna bayan sauya sheka. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook

An bukaci jama’a su haɗa kai da SDP

Shugaban ya bayyana cewa wannan sauya sheƙar alama ce ta gajiya da rashin shugabanci nagari da ƙuncin rayuwa da mutane ke fuskanta.

Ya ce SDP ita ce hasken maganin duhu da ke ɗauke da burin kawo ci gaba da haɗin kai a jihar Gombe da Najeriya gaba ɗaya.

Sannan ya jaddada cewa SDP na kara matsayi a matsayin babbar jam’iyyar da ke shirin kubutar da jihar Gombe daga wahala.

Dalilin komawar abokin takarar Atiku APC

A wani rahoton, kun ji cewa wanda ya yi takara da Atiku Abubakar a zaben 2023, Ifeanyi Okowa ya yi karin haske bayan sauya shekar da ya yi zuwa APC a makon da ya wuce.

A wani gagarumin taro da aka yi a jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya ce dole ne a rika samun sauyi a siyasa idan ana son samar da cigaba.

Okowa ya kara da cewa ya fita daga PDP ne zuwa APC saboda yadda suke kokarin kawo cigaba mai dorewa a jihar Delta wajen hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng