'Za Mu Kawo Kuri'ar Yankinmu,' Manyan Ibo Sun Yi Alkawari bayan Tinubu Ya Yi Masu Aiki
- Sarakunan gargajiya daga Kudu Maso Gabas sun ce za su ba Shugaba Bola Tinubu kaso mai tsoka na kuri’un da za a kada a zabe mai zuwa
- Sarakunan, a karkashin jagirancin Mai martaba Eze Nnamdi Odoregu sun dauki saboda kafar Hukumar Ci gaban Kudu Maso Gabas a yankin
- Sun yi addu’o’in samun nasara ga Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, saboda ayyukansu a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sarakunan gargajiya daga yankin kabilar Ibo da ke shiyyar Kudu maso Gabas sun sha alwashin ba wa Bola Tinubu akalla 70% na kuri’un yankin a zabe mai zuwa.
Sarakunan, a karkashin kungiyar Ndi Igbo Progressive Traditional Rulers Council, suna karkashin jagorancin Mai Martaba Eze Nnamdi Oforegbu daga jihar Abia.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa sun bayyana wannan matsaya ne a yayin wata ziyarar ban girma da suka kai wa Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Benjamin Kalu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin kabilar Ibo sun rungumi tafiyar Tinubu
Jaridar Leadership ta wallafa cewa, a madadin sauran sarakunan, Eze Oforegbu ya bayyana godiyarsu ga gwamnatin tarayya bisa kokarinta na kawo cigaba a yankin.
Sun yaba da kafa Hukumar Ci gaban Kudu Maso Gabas (SEDC) da Shugaba Tinubu ya yi, suna masu fatan hakan zai hanzarta gina muhimman ababen more rayuwa a yankin.
Sarakunan sun kuma yaba da kwazon Mataimakin Kakakin Majalisar, musamman yadda ya dauki nauyin kudirin da ya samaar da kafuwar wannan hukuma.
Shugabannin Ibo sun sa wa gwamnati albarka
Sarakunan gargajiyar sun yi addu’o’i na musamman tare da yi wa gwamnatin Tinubu albarka, suna rokon Ubangiji ya kara masa basira da ci gaba a harkar siyasa.

Asali: Facebook
Oforegbu ya ce:
“Mun zo nan ne don mu gode maka. Abin da kake yi ya wuce yadda muka yi tsammani. Wannan bai ya taɓa faruwa a da. Ba mu taba ganin irin wannan aiki ba.
“Kai ne ka dauki nauyin kudirin da ya sa aka kafa Hukumar Ci gaban Kudu Maso Gabas (SEDC). Wannan sabon abu ne a gare mu. Muna rokon Allah Maɗaukaki ya albarkace ka.
“Muna tabbatar masa da kuri’unmu – 70% a zabe mai zuwa. Muna ba ka tabbacin muna tare da kai. Ka ci gaba da samun nasara."
An bukaci Tinubu ya ajiye Shettima
A wani labarin, mun ruwaito cewa yayin da ake cigaba da shirye-shirye a kan zaɓen shekarar 2027, kungiyar matasan Arewa ta ba Bola Tinubu shawara don sake lashe zabe mai zuwa.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya zaɓi Kirista daga yankin Arewa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaben mai zuwa, maimakon ci gaba da tafiya da Kashim Shettima.
Kungiyar ta ce zaɓar Kirista Arewa a matsayin mataimaki zai taimaka wajen kawar da rashin daidaiton addini da ya jawo ce-ce-ku-ce bayan zaɓen 2023, zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng