A ƙarshe, Hakeem Baba Ahmed Ya Fadi Gaskiyar Dalilin Murabus a Gwamnatin Tinubu
- Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce bai jin ana bukatarsa a gwamnatin Bola Tinubu
- Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce shugaban kasa ba ya ba da lokaci ga masu taimaka masa domin tattauna wasu batutuwan jama'a
- Ya bayyana cewa bai taba samun damar zama da Tinubu ba duk da kasancewarsa mai ba shugaban kasa shawara kan siyasa
- Tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa ya ce shugabannin da ke kusa da Tinubu ba sa fahimtar halin da talakawa ke ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya fadi dalilin ajiye aikinsa .
Baba-Ahmed ya ce bai jin ana bukatarsa sosai a gwamnatin Bola Tinubu duba da rashin samun damar ganawa da shugaban kasar.

Asali: Twitter
Dalilin yin murabus na Hakeem Baba-Ahmed
Da yake magana a shirin Arise TV a jiya Litinin, Baba-Ahmed ya ce da aikin na kashin kansa ne kadai, da ya ci gaba da zama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baba-Ahmed ya ajiye aikinsa a fadar shugaban kasa a watan Maris din wannan shekara ta 2025.
Dattijon ya ce bai ci gaba da zama da muƙamin ba kuma yana ganin munanan abubuwa na faruwa a ce ba zai iya yin magana ba.
Ya ce:
"Da aikin na kaina ne kawai, mai yiwuwa da na ci gaba da zama, amma na ji zan fi amfani wa kasa da gwamnati.
"Ina kuma ganin, ba don na yi alfahari ba, amma ina ganin ina da abin bayarwa, domin dalilin da yasa aka ce in je can, ba don in zauna ina kallo abubuwa suna lalacewa ba.
"Ba ka da damar gyara su. Ba ka da damar tattaunawa da shugaban kasa wanda ke da dukkan ikon da ake bukata, babu wata hanya."

Asali: Facebook
Baba-Ahmed ya magantu kan haduwarsa da Shettima
Baba-Ahmed ya ce duk da cewa yana haduwa da Shettima kusan kowace rana, hakan bai wadatar ba, cewar TheCable.
"Ina ganin mataimakin shugaban kasa, ina ganinsa kusan kowace rana. Muna magana, muna tattaunawa kan kasa, amma Najeriya na bukatar fiye da hakan.
"Ina tunanin na gan shi (Tinubu), mun yi musabaha sau uku a masallacin fadar gwamnati. Amma ban taba samun damar zama da Shugaba Tinubu ba.
"Gaskiya ban sani ba. Ina ganin wani bangare na matsalar shi ne ba ya da lokaci ga mutane irina, ban tabbata yana da lokaci ga wasu da yawa da ke aiki a gare shi ba."
- Cewar Baba-Ahmed
Hakeem Baba-Ahmed ya sake sukar Tinubu
A wani labarin, tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya buƙaci Bola Tinubu da ya hakura da takara a 2027 domin bai wa sababbin hannu.
Hakeem Baba-Ahmed ya ce hakan zai ba Tinubu damar kafa kyakkyawan tarihi, yana mai gargadin cewa tsunduma cikin siyasar 2027 a yanzu na iya hana nasarar.
Dr. Baba-Ahmed ya soki salon shugabancin Tinubu, yana cewa yana da alaka da rashin jin daɗin al’umma, rashin tsari da kuma salon shugabancin nuna wariya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng